Abdussamad Rabiu Ya Samu Karuwar Arziki Zuwa Dala Biliyan 7 Bayan Rage Farashin Siminti Zuwa 3,500

Abdussamad Rabiu Ya Samu Karuwar Arziki Zuwa Dala Biliyan 7 Bayan Rage Farashin Siminti Zuwa 3,500

  • Mamallakin kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya kara samun ci gaba a fagen masu kudi a Nahiyar Afirka
  • Rabi'u ya samu ribar Dala miliyan 500 a watan jiya inda yanzu kudinsa ya kai fiye da Dala biliyan 7
  • Wannan karuwar arzikin bai rasa nasaba da rage farashin siminti da kamfanin ya yi wanda ya sauya akalar kasuwanci

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya sake samun riba inda kudinsa yanzu ya kai Dala biliyan 7.

Rahoton Forbes ya ce Rabiu yanzu ya samu karuwar ribar Dala miliyan 500 a watan da ya gabata bayan rage farashin siminti.

Rabiu ya samu karuwar arziki bayan rage farashin siminti
Mai kamfanin BUA ya kara sama a karuwar arziki. Hoto: BUA Group.
Asali: UGC

Wane matsayi BUA ya ke yanzu a jerin masu kudi?

A watan Satumba, Rabiu ya na da Dala biliyan 6.5 amma a yanzu ya haura har fiye da Dala biliyan 7.

Kara karanta wannan

An Kama Dan Kasuwa a Kano Kan Hada Baki Da Wasu Mutane 2 Don Yi Wa Abokinsa Fashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai kamfanin BUA yanzu haka shi ne na biyu a ma su arzikin Najeriya inda ya ke na biyar a Nahiyar Afirka.

Rahoton Billionaires Africa ya bayyana cewa Rabi'u ya samu kudaden ne saboda hannun jarinsa da ke kamfanin BUA na kaso 96 a matsayin silar karuwar arzikinsa.

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin ya rage farashin siminti wanda ya kara tagomashi a hannayen jari na kamfanin.

Meye ake hasashen jawo karuwar arzikin BUA?

Ana hasashen cewa rage farashin ya jawo mafi yawan kwastomomi zuwa siyan kaya wanda ya sauya akalar kasuwanci gaba daya.

Raguwar yawan kashe kudade ya jawo rage farashin zuwa Naira 3,500 da kamfanin ya yi, Legit ta tattaro.

Masana sun ce hakan na iya taba samar da kudin shiga na kamfanin amma zai kara wa kamfanin da masu hannun jari tagomashi na riba.

Kara karanta wannan

Najeriya ta Samu Dama Bayan Karya Tarihin Tsawon Shekara 60 a Bankin Duniya

A bangarenshi, Aliko Dangote ya karyata jita-jitar cewa ya rage farashin siminti a kamfaninsa zuwa kasa da Naira dubu uku.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu kan wannan lamari na BUA:

Isma'il Muhammad ya ce tabbas ya ji dadin wannan abin da ya ji saboda Allah shi ke ba da arziki ba tsadar kaya ba.

Bashir Umar ya ce:

"Na yi masa murna, amma tsakani da Allah ba mu ga inda ake siyar da simintin kamar yadda ake fada ba."

Wani da ya boye sunansa ya ce:

"Wannan ya zama wa'azi ga Dangote shi ma idan ya na son arzikinsa ya karu ga hanya mafi sauki."

Kamfanin BUA ya rage farashin siminti zuwa Naira 3,500

A wani labarin, shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya sanar da rage farashin siminti a Najeriya zuwa Naira 3,500 a kamfani.

Kamfanin ya dauki wannan matakin ne don tabbatar da samun sauki a kasar inda ya ce dokar ta fara aiki tun 2 ga watan Oktoban wannan shekara da mu ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel