'Yan Kwadago Sun Yi Fatali da Mafi Ƙarancin Albashin da Gwamnatin Tinubu Ta Gabatar

'Yan Kwadago Sun Yi Fatali da Mafi Ƙarancin Albashin da Gwamnatin Tinubu Ta Gabatar

  • Ƙungiyoyin ma'aikata a Najeriya sun yi fatali da sabon mafi ƙarancin albashi wanda gwamnatin tarayya ta gabatar masu yau Laraba
  • Gwamnatin ta ba da shawarar a ƙara mafi ƙarancin albashin daga N30,000 zuwa N48,000 a taron kwamitin da aka kafa a Abuja
  • Sai dai kungiyoyin ma'aikata NLC da TUC sun nuna rashin amincewa da adadin, inda suka fice daga taron wanda ya gudana ta intanet

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƴan kwadago a Najeriya sun yi fatali da N48,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati a ƙasar nan.

Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta gabatar da wannan adadi a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ne a wurin taron kwamitin da aka kafa.

Kara karanta wannan

"Ba ka da lissafi ko kadan": Kungiyar TUC ta ɗaga yatsa ga Tinubu kan karin albashi

Yan kwadago a Najeriya.
Kungiyoyin kwadago sun fice daga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi cikim fushi Hoto: Nigeria Labour Congress
Asali: Twitter

Rahoton The Nation ya tattaro cewa kwamitin da aka kafa da nufin lalubo matsaya guda kan albashin ma'aikatan ya ci gaba da zama yau Laraba, 15 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC da TUC ba su amince da N48,000 ba

Domin nuna adawa da N48,000 da gwamnati ta gabatar, manyan ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC sun fice daga taron cikin fushi tun kafin a gama.

Wani jagoran ’yan kwadago da ya samu halartar taron ya ce ga dukkan alamu gwamnatin tarayya ba da gaske take ba wajen bai wa ma’aikata albashin da za su rayu.

“Abin da gwamnati ta gabatar mana tamkar rage albashi ne. Wannan gwamnati ba da gaske take ba wajen bai wa ma’aikata albashin da zai riƙe su a yanzu,” in ji shugaban kwadagon.

Alkawarin da Tinubu ya yi wa ma'aikata

Kara karanta wannan

Kwamishina na 4 ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tura wasiƙa ga Gwamna Fubara

A ranar ma'aikata ta duniya a watan Mayu, Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin zuwa da albashin da zai ɗauki nauye-nauyen ma'aikatan gwamnati, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma tabbatarwa ma'aikata cewa dakon da suke na jin sabon mafi ƙarancin albashi ya zo ƙarshe domin nan ba da jimawa ba za su san matsayar da aka cimma.

NLC da TUC sun gabatar da shawarar N615,000 a matsayin mafi karancin albashi, bisa la’akari da tsadar rayuwa a matsayin ma’aunin da ya kamata a duba.

Wani ma'aikacin gwamnatin tarayya, Nura Muhammad Aliyu, ya nuna rashin jin daɗinsa da wannan adadi na N48,000, inda ya ce bai taɓa tsammani ba.

Ya shaida wa Legit Hausa cewa mafi yawan ma'aikata sun yi tsammanin mafi ƙarancin albashi sai ya nunka tsohon akalla duba da tsadar da rayuwar da aka shiga.

Ya ce:

"Ina tare da kungiyoyin mu, wallahi wannan bai kama da halin da ake ciki, idan ka duba komai ya nunka sau ɗaya, biyu wani ma sau uku, ina ake son mu sa kanmu?"

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa na ƙona mutane suna sallah a Kano," Wanda ake zargi ya faɗi gaskiya

Gwamnatin Tinubu na shirin kashe kudin fansho

A wani rahoton na daban gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta fara shirin kashe kuɗin ƴan fansho domin gudanar da wasu ayyuka.

Ministan kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron FEC na kwanaki biyu a fadar shugaban ƙasa ranar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel