BUA Ya Sake Shiga Jerin Masu Kudin Duniya 500 Bayan Cin Ribar Naira Miliyan 986 A Kwana 1

BUA Ya Sake Shiga Jerin Masu Kudin Duniya 500 Bayan Cin Ribar Naira Miliyan 986 A Kwana 1

  • Abdussamad Rabiu wanda shi ne na biyu mafi kudi a Najeriya ya sake samun karin mataki a duniyar jerin masu kudi
  • Rabi'u ya samu shiga jerin masu kudin duniya 500 sanadin samun kazamar riba a cikin sa'o'i 24
  • Duk da ribar da Rabiu ya samu, amma ya na baya idan aka kwatanta da Dangote da sauran 'yan Afirka da ke jerin masu kudin 500

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Abdussamad Rabiu ya sake shiga jerin masu kudin duniya tare da Aliko Dangote.

Rahoton Bloomberg ne ya tabbatar da haka inda ya ce Abdussamad Rabiu ya samu kazamar riba a cikin sa'o'i 24.

BUA ya matsa kusa da Dangote, ya ci ribar miliyan 986
BUA Ya Ci Ribar Naira Miliyan 986 Miliyan 986 A Kwana 1. Hoto: Bloomberg/Contributor.
Asali: Facebook

Ribar nawa BUA ya samu a sa'o'i 24?

Rabi'u ya fice daga jerin masu kudin tun a watan Yuni na 2023 bayan durkushewar darajar Naira a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jirgi ya Kama Ci da Wuta Za Ayi Tafiya, Gwamna da Hadimansa Sun Tsira Daga Hadari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A 'yan kwanakin nan, Rabiu ya samu ci gaba inda ya hauro matakin masu kudin na duniya 500.

Rahoton ya ce Rabiu ya samu ribar Naira miliyan 986 a cikin sa'o'i 24 inda darajar kudinsu ya kai Dala biliyan 5.18 a yau Litinin 18 ga watan Satumba.

Bloomberg ya bayyana Rabiu a matsayin mafi kudi a duniya a mataki na 500, Legit ta tattaro.

Rabiu shi ne mai kamfanin BUA wanda a hada kamfanoni da dama a fadin kasar, kamfaninsa na siminti a Legas shi ne na biyu mafi girma a fadin Najeriya ba ki daya.

Jerin masu kudin da BUA ke ciki

Arzikin Rabi'u idan aka kwatanta da takwarorinsa a Afirka

1. Aliko Dangote - Dala biliyan 17.5 (Najeriya)

2. Johann Rupert - Dala biliyan 11.6 (Afirka ta Kudu)

Kara karanta wannan

Shin Wannan Na Daga Cikin Amfanin Cire Tallafi? NNPC Ya Bayyana Tsurar Ribar Da Ya Samu A Watanni 3

3. Nicky Oppenheimer - Dala biliyan 9.25 (Afirka ta Kudu)

4 Nassef Sawiris - Dala biliyan 7.67 (Masar)

5. Natie Kirsh - Dala biliyan 7.27 (Afirka ta Kudu)

6. Naguib Sawiris - Dala biliyan 5.84 (Masar)

7. Abdulsamad Rabiu- Dala biliyan 5.18 (Najeriya)

Kamfanin BUA Ya Shirya Rage Farashin Siminti A Najeriya

A wani labarin, Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya ce sun shirya tsaf don rage farashin siminti a fadin Najeriya.

Kamfanin ya ce zai yi hakan ne don dafa wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu wurin inganta tsare-tsarensa na ci gaban tattalin arziki

Asali: Legit.ng

Online view pixel