NNPC Ya Fadi Gaskiyar Abin da Ya Jawo Ake Ganin Layin Fetur a Gidajen Mai

NNPC Ya Fadi Gaskiyar Abin da Ya Jawo Ake Ganin Layin Fetur a Gidajen Mai

  • Malam Mele Kolo Kyari ya alakanta dawowar layi a gidajen mai da wahalar da direbobin motoci su ke sha a kasar
  • Baya ga tare wasu hanyoyi da ake yi, NNPCL ta ce jama’a su na cincirindo ne a gidajen man da su ka fi arahar fetur
  • Kamfanin NNPCL ya tabbatar da cewa a yanzu shi kadai ya ke shigo da fetur saboda wahalar samun kudin ketare

Abuja - Mele Kolo Kyari wanda shi ne shugaban kamfanin mai na NNPCL ya yi bayanin abin da ya jawo dawowar layi a gidajen man fetur.

Da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, Daily Trust ta ce Mele Kolo Kyari ya nanata cewa akwai isasshen man fetur a kasa.

Fetur
Shugaban kamfanin man fetur na NNPCL, MKKyari Hoto: NNPCLimited
Asali: Twitter

Matsalar hanya da tashin Dalar Amurka

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

A jawabin da ya yi a Abuja a ranar Litinin, Mele Kyari ya alakanta lamarin da toshe tituna da ake yi, ya ce hakan ya sa direbobi yin zagaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kamfanin na NNPCL ya yi magana game da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin ‘yan kasuwa sun samu dala da sauki.

Idan ana samun dala a kafar CBN na I & E a kan N770, dillalai za su iya shigo da fetur, amma yanzu NNPCL kadai ke kawo mai cikin Najeriya.

Bayanin Shugaban NNPCL kan wahalar fetur

"Mu na ganin layi kadan a wasu daidaikun jihohi. Wannan bai rasa nasaba da halin da tituna ke ciki
Mu na ganin ana tare kaya daga tashoshin kudu zuwa na yankin Arewa, hakan ya jawo ana cin lokaci.
Dole su canza hanya da motocinsa wanda hakan ya yi sanadiyyar bata lokaci da kuma matsalar gas.

Kara karanta wannan

Ministan APC Ya Ambaci Kura-kurai 2 da Tinubu Ya Tafka Daga Hawa Kan Mulki

Amma an magance wannan yanzu, saboda haka ba za mu sake samun matsalar nan ba."

- Mele Kolo Lyari

Dalili na biyu shi ne karin da wasu gidajen mai su ka yi ya jawo mutane su na rububi a gidajen da ba su canza farashi ba a cewar NNPCL.

Man fetur zai kara kudi?

Tun a makon jiya mu ka fara kawo maku rahoton yadda fetur ya fara yin wahala baya ga tsada da mutane su ke kukan mai ya yi a yau.

An fahimci farashin da ake sayen man fetur a tasoshi ya tashi daga kusan N650 zuwa N720, hakan ya sa ake zargin an dawo da tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel