Man Fetur Zai Kara Tsada a Gidajen Mai Tun da Farashi a Tashoshi Ya Zarce N720

Man Fetur Zai Kara Tsada a Gidajen Mai Tun da Farashi a Tashoshi Ya Zarce N720

  • ‘Yan kasuwa da dillalai sun shiga mawuyacin hali a yau a sakamakon tashin farashin litar fetur
  • Maganar da ake yi, farashin da ake sayen man fetur a tasoshi ya tashi daga kusan N650 zuwa N720
  • Canjin ya yi sababin rufe wasu gidajen mai, hakan zai jawo a koma zamanin wahalar mai a Najeriya

Abuja - A halin yanzu, ‘yan kasuwa da dillalai da-dama sun kaurcewa tashoshin mai, hakan bai rasa alaka da tsadar da man fetur ya kara yi.

Rahoto ya fito daga Punch a ranar Juma’a cewa akasarin abin da ake saida duk litar man fetur a manyan tashoshin kasar nan ya kai N720.

Wannan ya jawo ‘yan kasuwa da yawa sun rufe gidajen mansu a sakamakon yankewar man fetur kamar yadda aka fara samun labari.

Kara karanta wannan

An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615 da Attajiri Ya Tausayawa Mutanen Kano

Man Fetur
Motoci na neman fetur Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Layin fetur zai dawo gidajen mai?

Idan abubuwa ba su canza ba, wannan lamarin zai iya jawo wahalar man fetur, abin da ba a sake gani ba tun bayan janye tsarin tallafin mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga akalla N650 da aka rika sayen mai a tashoshi a watan Agusta, yanzu litar fetur ta koma N720, hakan ya na nufin an samu kari na N70.

"Kasuwa ta yi wahala" - NOGASA

Shugaban kungiyar NOGASA ta masu samar da mai da gasa Najeriya, Benneth Korie ya shaida cewa kayansu sun fara karewa a halin yanzu.

Da yake magana a garin Abuja a jiya, Korie ya nuna tashin kudin kasar waje da tsadar da fetur ya kara ya jawo karancin man fetur a tashoshin.

Bayan haka, ‘dan kasuwan ya ce tulin ruwa da bankuna su ke narkawa ya na hana su iya cin bashi.

Kara karanta wannan

An Koma Gidan Jiya, Fetur Ya Fara Wahala, Farashi Ya Haura N650 a Gidajen Mai

"Bankuna ba su da niyyar ba ‘yan kasuwa kudi a dalilin wahalar da ake ciki; rashin tabbas, tashin kudin kasar waje da tsadar Dala.
Tasoshi da yawa sun bushe ko kuma babu mai, a bayyana yake cewa kowa za iya ganin haka.
Wadanda abin ya fi shafa su ne masu gidajen mai wanda ba su iya samun kudi daga banki, abin da ya shafi duka ‘yan kasuwa sosai."

- Benneth Korie

Za a fara wahalar man fetur?

Da Legit ta tuntubi masu motoci a garin Minna, an ji cewa har yanzu ana samun mai da araha; N614 (NNPC), N617 (Gidan man AYM Shafa).

Wani ma'aikacin banki da ke aiki a Kaduna, ya fada mana a gidan man NNPC ana samun mai har cikin dare a kan farashin gwamnati.

Attajiri ya karya kudin fetur

Farashin man fetur ya karye da N200 a kowane lita yayin da wani attajiri ya saukakawa jama’a kamar yadda aka samu labari a jiya.

Ibrahim Jibrin Mohammed ya bude gidan mai ya kuma saidawa mutane da araha, hakan ya sa motoci sun cika domin sayen fetur a N415.

Asali: Legit.ng

Online view pixel