Ministan Buhari Ya Ambaci Kura-kurai 2 da Tinubu ya yi Daga Hawa Kan Mulki

Ministan Buhari Ya Ambaci Kura-kurai 2 da Tinubu ya yi Daga Hawa Kan Mulki

  • Solomon Dalung ya na ganin babu tausayi a tsare-tsaren da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo
  • Idan har ba a dauki matakin gyara ba, tsohon Ministan ya ce shugaban kasar zai samu matsala
  • Dalung bai goyon bayan cire 100% na tallafin fetur da barin darajar Naira a hannun ‘yan kasuwa

Abuja - Tsohon ministan wasanni da matasa na kasar nan, Solomon Dalung ya zargi Bola Ahmed Tinubu da fadawa tarko.

A ranar Lahadi, Daily Trust ta rahoto ‘dan siyasar ya na cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi kuskuren janye tallafin man fetur.

Da aka yi wata hira da shi a karshen makon jiya, Dalung ya tofa albarkacin bakinsa a kan gwamnatin baya da kuma mai-ci.

Bola Tinubu
Solomon Dalung ya yi kira ga Bola Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya jawo tsadar man fetur

Hon. Dalung ya na ganin katabora aka tafka da shugaba Tinubu ya yi watsi da tsarin tallafin fetur da aka dade ana mora.

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janye tallafin ya jawo farashin man fetur ya tashi daga kusan N180 zuwa kusan N700 a 'yan kwanakin bayan nan.

"Ya yi babban kuskure da ya fada tarkon masu ci da tallafin fetur, da ya yi jawabi ya na cewa tallafi ya tafi kenan.
Har yanzu mutanen Najeriya ba su farfado daga wannan hali da su ka shiga ba."

- Solomon Dalung

Idan har dole sai an janye tallafin man fetur a kasar, tsohon ministan matasa da wasannin ya na ganin bai dace a janye duka ba.

A hirarsa da tashar rediyon Trust, lauyan ya kawo shawarar a bar 50% na tallafin da ake amfana, sai man fetur ya tashi da 50%.

Tashin Dalar Amurka

Da aka zo kan batun Naira, nan ma tsohon ‘dan takaran gwamnan na APC ya nuna akwai bukatar a a tsare darajar kudin kasar.

Kara karanta wannan

Litar Mai N620: A Hakan, Gwamnati Ba Ta Janye Tallafin Man Fetur – PENGASSAN

A ra’ayin Dalung, ba daidai ba ne a bar Naira ta rika gantali a kasuwa, ya ce yin hakan tamkar tura soja yaki ne babu makami.

“Dole ya ceci al’umma tukun kafin kawo manufofin tattali, kyau manufofinsa su tausayawa jama’a, ko ya zama irin Buhari.”

- Solomon Dalung

Gwamnati ta hana a tafi yajin-aiki

Kwanaki kun ji yarjejeniyar gwamnatin tarayya da 'yan kwadago sun hada da karin N35, 000 a albashi da kokarin rage farashin dizil.

Kwamred Joe Ajaero, Kwamred Emmanuel Ugboaja, mni, Injiniya Festus Osifo da Kwamred Nuhu A. Toro su ka wakilci ‘yan kwadago.

Asali: Legit.ng

Online view pixel