Takaitaccen tarihin sabon shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari
A ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da nadin Mele Kolo Kyari a matsayin sabon manajan darakta na kamfanin NNPC.
Mista Kyari wanda ya fito daga jihar Borno, zai maye gurbin manajan daraktan kamfanin mai ci, Maikanti Baru, wanda zai yi ritaya daga kamfanin NNPC a wata mai zuwa.
Kyari, ya kammala digirin sa na farko a Jami’ar Maiduguri cikin 1987, inda ya karanci fannin Nazarin Albarkatu da Kimiyyar Karkashin Kasa.
Ya kuma kasance kwararren masani harkokin man fetur, inda ya shafe shekeru 32 ya na aikin harkokin danyen mai da albarkatun kasa.
Ya yi aiki a bangarori da dama, kuma ayyukan sa sun rika yin tasiri a sauran bangarorin NNPC.
Sabon shugaban na NNPC ya taka rawar gani wajen samar da ingantaccen sauyin ciniki da hada-hadar danyen man fetur, ta hanyar gudanar da harkokin tafiyar da kasuwancin a bisa ka’ida, ba tare da kumbiya-kumbiya ba.
Ya yi aikin bautar kasa (NYSC) a Hukumar Inganta Abinci da Titinan Raya Karkaka (DFRRI), a cikin 1987 zuwa 1988.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a kamfanin NNPC, Kyari ya zama manajan darakta
Kafin nadin Kyari, ya kasance babban Janar Manaja mai kula da Bangaren Kasuwaci da Cinikin Danyen Mai.
Kuma tun daga watan Mayu 2018 aka kara masa matsayi inda ya shi ne Wakilin Najeriya a Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC).
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng