“Karamar Barauniya”: Matashi Ya Fusata Bayan Budurwa Ta Karbi Kudin Mota a Hannunsa Amma Ta Ki Zuwa
- Wata matashiya yar Najeriya ta yi fice a soshiyal midiya bayan ta saki sakon WhatsApp da wani mutum ya aike mata
- A cikin sakonsa, mutumin ya kira ta da "karamar barauniya" kan ta ki kai masa ziyara bayan ya tura mata da kudin mota
- Lamarin ya kayatar da mutane inda suka garzaya sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu
Wata yar TikTok mai suna @_halfgirlfriend ta saki hoton hirarsu da wani mutumi wanda ya aika mata da kudin mota.
Sai dai kuma, da gangan ta ki zuwa kuma hakan ya fusata matashin wanda ya yi martani nan take.
Matashi ya ji radadi bayan matashiyar da ya aikawa kudin mota ta ki zuwa
Mutumin ya aika mata da sako ta WhatsApp yana mai bayyana rashin jin dadinsa kan abun da ta yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Kin ba ni kunya, ke yar karamar barauniya."
Martanin jama'a kan budurwar da ta karbi kudin mota amma ta ki zuwa wajen saurayi
@top LIVE ta ce:
"Yan uwa mata na alfahari da ke."
@Nancy Andrew ta ce:
"Abun ya yi masa ciwo."
@lovelylo400 ta yi martani:
"Koya mani dabarar."
@mima ta yi martani:
"A kowani dan lokaci."
@Ashleyyyy ta yi martani:
"Yarinya ina bukatar sanin ko kin mayar da shi."
@Best ta yi martani:
"Kada akpi ya ga wannan bidiyon."
@Ibunkun ya ce:
“Baba na so ya yi kuka."
Kalli wallafar a kasa:
Ya cika mako: Budurwa ta ba da labarin yadda ta kare bayan ziyartar saurayinta
A wani labarin, wata budurwa a Najeriya ta koka kan yadda tayi tafiya mai dogon zango daga Jos har jihar Lagos don kai ziyara wurin saurayinta.
Ta bayyana saurayin nata a matsayin mutum mai mako bayan ta share kwanaki a gidansa amma ko kudin mota ma bai bata ba.
Ta ce lokacin da take gidan nasa, ta kwanta jinya kuma ita tayi wa kanta magani da kudinta tun da saurayin bashi da niyyar taimakonta.
Ta ce matsalarta da saurayin shine, duk lokacin da tace tana son cin kifi ko shawarma sai yace ta kawo kudin don babu kudi a wurinsa, ta ba shi ya siyo musu amma zai fi ta ci da yawa.
Asali: Legit.ng