Budurwa Ta Hadu Da Saurayin Da Ya Yi Tattaki Daga Amurka Don Ganinta a Karon Farko

Budurwa Ta Hadu Da Saurayin Da Ya Yi Tattaki Daga Amurka Don Ganinta a Karon Farko

  • Wani bidiyo mai tsuma zuciya na budurwa yar kasar Uganda da ta hadu da masoyinta na soshiyal midiya ya yadu
  • Matashin ya yi tattaki daga kasar Amurka domin yi mata bazata, kuma sun rungume juna cike da shauki a filin jirgin sama
  • Matashiyar ta ce sun hadu ne a dandalin kulla soyayya ta yanar gizo, kuma soyayyarsu ta yi zurfi

Wani bidiyo mai taba zuciya na wata mata yar kasar Uganda da ta yi ido hudu da saurayin da suka hadu a intanet ya tsuma zukata a soshiyal midiya.

Masoyin nata ya yi tattaki daga kasar Amurka domin kai mata ziyarar bazata, kuma sun rungume junansu cike da shauki a filin jirgin sama.

Matashi ya yi tattaki daga Amurka don ganin budurwa
Budurwa Ta Hadu Da Saurayin Da Ya Yi Tattaki Daga Amurka Don Ganinta a Karon Farko Hoto: TikTok/@wizzydesire
Asali: TikTok

Sun kuma bi haduwar tasu da zazzafar sumba da ke nuna yadda suke kewar junansu duk da cewar basu taba haduwa ba.

Kara karanta wannan

Namijin Duniya: Wani Dattijo Ya Tsara Budurwa a Waya, Ya Yi Alkawarin Mallaka Mata Zuciyarsa Kacokan

Matar ta bayyana cewa sun hadu ne a wani dandalin kulla soyayya na yanar gizo sannan shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu inda daga bisani ya juye ya zama so.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa sun dade da fara magana a tsakaninsu sannan sun yanke shawarar kai soyayyar tasu zuwa mataki na gaba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

AmondiAroko ta ce:

"A karshe soyayyar wasu bakaken fata."

User3420295977640 ta rubuta:

"Na taba sauke wani manhajar soyayya sannan bayan na shiga sai na ga kajoba. Makwabcinmu ne a nan."

youngest...realtor ya yi martani:

"Tunanina na ta fada mun yadda za su shafe dare kacokan suna morar juna."

Kakamorenike:

"Aoyayyar soshiyal midiya ba na masu raunin zuciya bane...idan ka san baka da karfi sosai don Allah kada ma ka fara a bangarena na gama da soyayyar soshiyal midiya ba zan zo na mutu ba."

Kara karanta wannan

“Na Saduda”: Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Ci Kudinta a Gidan Caca, Bidiyon Ya Taba Zukata

isabella Mars:

"Da gaske ne amma yana da wahala samun dan gaske."

Lissa123"

"Na kagu na samu nawa nima."

Bidiyon wani dattijo yana tsara budurwa ya girgiza intanet

A wani labarin, bidiyon wani dattijo dan kasar Ghana yana tsara budurwarsa da kalamai masu dadi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

An gano dattijon yana kokarin shawo kan matashiyar a wayar tarho, tare da fada mata irin sadaukarwar da ya yi don tabbatar da son da yake yi mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng