Allah Ya Yi wa Gwamna da Hadimai Gyadar Dogo Sun Tsallake Hadarin Jirgin Sama

Allah Ya Yi wa Gwamna da Hadimai Gyadar Dogo Sun Tsallake Hadarin Jirgin Sama

  • Gwamnan jihar Osun ya na cikin jirgin Bombadier Global Express 6000 da ya samu cikas a Legas
  • Mutane na shirin tashi daga birni Legas zuwa birnin Abuja, sai aka ji fashewar wani a jirgin saman
  • Zuwa yanzu ba a samu labarin wanda ya samu rauni da abin ya auku ba, duka fasinjojin sun tsira

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Ubangiji ya nufa da sauran kwana, amma da labarin ya yi muni yayin da jirgin Adedeji Adeleke ya kama ci da wuta a filin jirgi.

A safiyar Lahadi, Leadership ta fitar da rahoto cewa jirgin saman da Cif Adedeji Adeleke ya mallaka, ya samu matsala a lokacin da za a tashi.

Abin ya faru a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Innalillahi, Bene Mai Hawa 20 Ya Rushe Kan Jama'a a Babban Birnin Jihar PDP

Hadarin Jirgin Sama
Gwamnan Osun ya na cikin jirgin Bombardier Global Express Hoto: ultimatejet.com
Asali: UGC

Saura kiris jirgin sama ya jawo matsala

Yayin da jirgin ya ke shirin barin filin MMIA a Legas zuwa birnin Abuja da safiyar Asabar da kimanin karfe 9:00, sai aka samu tangarda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

To sai dai, rahoton ya ce ba a sanar da hukumomin da ke kula da sha’anin jiragen sama a Najeriya ba, wanda hakan ya sabawa tsari da ka’ida.

Gwamna Ademola Adeleke da wasu daga cikin manyan mukarrabansa su na cikin wadanda za su yi tafiya, su na daf da tashi daga tashar jirgin.

Yadda abin ya faru a tashar jirgin Legas

Kwatsam sai aka ji wani kara daga injin jirgin saman a daidai lokacin da za a tashi sama. Labarin nan ya zo a shafin nan na Linda Ikeji dazu.

Zuwa yanzu majiyoyi sun ce babu labarin rauni da aka samu ko rai da aka rasa a sanadiyyar lamarin, ana sa ran duk fasinjojin sun tsira.

Kara karanta wannan

Azarɓaɓin Hadimin Tinubu Ya Jawo An Ji Kunya, Gwamnati Tayi Ƙarya a Ƙasar Waje

Shugaban kamfanin jirgin, Sam Iwuajoku ya shaida cewa jirgin ya na ajiye ne tun tuni domin ya da wata matsala da ke jawo saurin daukar zafi.

Jirgin saman Ademola Adeleke

Adeleke shi ne mahaifin David Adeleke wanda mutane su ka fi sani da Davido, shahararren mawaki ne wanda ake ji da shi a Afrika.

Baya ga haka, ku na da labari attajirin ‘danuwa ne ga gwamnan jihar Osun watau Mai girma Ademola Adeleke wanda yake mulki tun 2022.

Babban 'dan kasuwan ya na da jirgin yawo kirar Bombadier Global Express 6000 wanda shi da mutanen danginsa su ka saba tafiya da shi.

Kamfanin Bombardier Aviation ya kere wannan jirgi tun shekaru 27 da su ka wuce, ko da yake bai fara tashi a duniya ba sai a tsakiyar 1999.

Asali: Legit.ng

Online view pixel