'Yan Majalisa Sun Fusata Kan Kashe Naira Biliyan 81 Wajen Dashen Bishiyoyi A Arewacin Najeriya

'Yan Majalisa Sun Fusata Kan Kashe Naira Biliyan 81 Wajen Dashen Bishiyoyi A Arewacin Najeriya

  • Kwamitin kula da asusun raya muhalli a majalisar wakilai ya fara bincike kan zargin badakalar kudade a shirin dashen itatuwa
  • Shirin dashen itatuwan karkashin Great Green Wall Project ta bai wa jihohin Arewa 11 damar dasa itatuwa miliyan 21
  • Daga cikin cikin jihohin da aka zaba akwai Gombe da Yobe da Adamawa da Borno da Jigawa da Kano da sauransu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai a Najeriya ta nuna bacin ranta yadda aka kashe biliyan 81 wurin dashen itatuwa a Arewacin Najeriya.

Kwamitin da ke kula da asusun raya muhalli da alkinta yanayi ya fara bincike kan zargin kashe biliyoyin kudade a kan lamarin.

Majalisar wakilai ta fara bincike kan kashe biliyan 81 don dashen Itatuwa a Arewacin Najeriya
'Yan Majalisa Sun Fusata Kan Kashe Biliyoyi A Dashen Bishiyoyi. Hoto: NASS TV.
Asali: UGC

Me majalisar ke zargi kan dashen Itatuwa?

Ana zargin hukumar da kashe biliyan 81 a dashen itatuwa miliyan 21 a jihohin Arewa wanda ke karkashin shirin Great Green Wall Project, The Guardian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Jama'a Sun Farmaki Rumbun Abinci A Wata Jiha, Sun Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maina Yusuf Bukar, wanda shi ne daraktan Hukumar ta NAGWW, ya bayyana sabanin abin da ake yadawa, ya ce sun kashe Naira miliyan 697.71 wajen gyara ofishin hukumar.

Yayin da kuma fiye da Naira biliyan 11 aka kashe su wurin aiwatar da manyan ayyukan hukumar.

Martanin hukumar kan zargi a dashen Itatuwa

Maina ya ce mafi yawan kudaden da hukumar ke samu sun fito ne daga asusun alkinta yanayi da muhalli sai kuma wadanda Gwamnatin Tarayya ke samar musu.

Jihohin da shirin ke gudanar da aikin sun hada da Kano da Jigawa da Zamfara da Katsina da Kebbi, cewar Daily Trust.

Sai kuma Sokoto da Bauchi da Gombe da Adamawa da Yobe da kuma Borno wadanda mafi yawansu ke kan iyakar Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan korafe-korafe kan makudan kudade da aka salwantar kan dashen itatuwan a jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Ibrahim Geidam: Muhimman abubuwa 6 da baku sani ba game da ministan harkokin 'yan sanda

Hakan ne ma ya jawo fara bincike daga kwamitin wanda ke da alhakin kula da asusun raya muhalli da alkinta yanayi.

'Yan Majalisa Za Su Samu N150m A Rabon N54bn Na Ayyuka

A wani labarin, ko wane dan majalisar wakilai a Najeriya zai samu Naira miliyan 150 daga cikin kudaden da za a raba na ayyuka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan na daga cikin Naira biliyan 54 da za a raba don ayyukan mazabu a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel