Hukuncin Kisa: Abduljabbar Kabara Ya Sake Korar Lauyansa Ana Cikin Shari’a

Hukuncin Kisa: Abduljabbar Kabara Ya Sake Korar Lauyansa Ana Cikin Shari’a

  • Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya kori lauyan da ke karesa a kotun daukaka kara yayin da ake sauraron shari'arsa da gwamnatin jihar Kano
  • Lauyan gwamnatin jihar Kano ne, Bashir Saleh ya yi nuni da haka tare da gabatar da takardar da malamin ya sa hannu kan korar lauyan nasa
  • Bayan sauraron korafi daga ɓangaren lauyan gwamnatin, alkalin kotun, mai shari'a Nasiru Saminu ya daga shari'ar har zuwa wani lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar kano - A yau Laraba ne, 15 ga watan Mayu kotun daukaka kara da ke Kano ta cigaba da sauraron karar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar a gabanta.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Ganduje zai sarara bayan kotu ta dakatar da bincikensa

Kabara
Kotu ta daga shari'ar Abduljabbar bayan ya kori lauyansa. Hoto: Politics Digest
Asali: UGC

Shari'ar Abduljabbar Kabara a kotu

Malam Abduljabbar Kabara ya daukaka kara ne biyo bayan hukuncin kisa ta hanyar rataya da wata kotu ta yanke masa bisa batanci ga Annabi (SAW).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa yayin zaman kotun na yau an samu tsaiko bayan an gano malamin ya kori lauyan da yake kare shi.

Yadda Abduljabbar Kabara ya kori lauyansa

A zaman kotun da ya gabata, Malam Abduljabbar Kabara ya shigar da ɗaukaka kara ne ta hannun lauyansa mai suna Sadiq Yusuf.

Sai dai lauyan wadanda ake kara, Barista Bashir Saleh ya tabbatarwa kotun cewa malamin ya dakatar da lauyansa da kansa.

Abduljabbar Kabara ya kori lauyansa ne a ranar Jumu'ah, 10 ga watan Mayu kamar yadda wata takarda ta tabbatar da hakan.

Meya faru bayan korar lauyan Abduljabbar?

Biyo bayan haka, lauyan gwamnatin Kano ya bukaci a cigaba da sauraron shari'ar ko da malamin bai da lauya mai kare shi.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Amma alkakin kotu bai amince da rokon ba kuma ya daga shari'ar zuwa ranar da Abduljabbar Kabara zai samo wani lauyan.

CBN ya koka da jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban bankin CBN reshen Kano Alhaji Umar Ibrahim Biu ya roki bankuna a jihar su shiga tsarin bayar da rance ga manoma.

Shugaban babban bankin ya ce rokon ya zama wajibi duba da cewa kananan bankunan masana’antu ne kadai ke taka rawa a cikin tsarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel