'Yan Gidan Magajiya Sun Shiga Dimuwa a Kano, Kwastomomi Sun Rage Zuwa Tun Bayan Cire Tallafin Mai

'Yan Gidan Magajiya Sun Shiga Dimuwa a Kano, Kwastomomi Sun Rage Zuwa Tun Bayan Cire Tallafin Mai

  • 'Yan gidan magajiya sun koka kan yadda tattalin arzikin Najeriya yake karyewa da kuma yadda suke talaucewa
  • Cire tallafin man fetur ya jawo kasuwanni da masu sana'a a Najeriya sun shiga wani yanayin da ke da ban takaici
  • Tun ranar da aka rantsar da shugaba Tinubu ya alanta janyewa 'yan kasar tallafin man fetur saboda wasu dalilai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Tabarbarewar tattalin arziki sakamakon cire tallafin man fetur ya yi matukar tasiri ga karuwai a jihar Kano yayin da suke koka kan rashin samun kwastomomi a yanzu, Vanguard ta tattaro.

Sun bayyana bacin ransu ne a lokacin da suke amsa tambayoyi wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge a ranar Lahadi.

Karuwan a cikin tsohon birni Kano, wadanda a baya suke cike aljihu da kudi tare da yanga yanzu sun koma neman abokan assha ido rufe saboda tsananin talauci.

Kara karanta wannan

"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

Yadda tsadar man fetur ya daidaita sana'ar karuwanci
Karuwai sun fara kukan rashin sana'a a Kano | Hoto: Vanguard News
Asali: Facebook

Yadda matsin tattalin arziki ya shafi karuwai a Kano

Mercy Benjamin ta shaida wa NAN cewa kafin yanzu, a baya suna samun kwastomomin wucin gadi d ake iya ba da N5,000 kowanne awa daya, amma banda yanzu da aka cie tallafin mai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta kara da cewa, a yanzu kwastomomin ba sa biyan sama da N500 zuwa N700 a kowane awa daya tsabar fatara.

Wata 'yan gidan magajiya, wacce ta bayyana kanta da Jennifer, ta shaida wa NAN cewa yanzu dai harkar ta su ba ta kawo wuta, komai ba ya motsi a bangarensu.

Kwastoman N20,000 sun koma ba da N1,500

Ta kuma bayyana cewa, akwai kwastomomin da a baya ke biyansu N20,000 a kwana dasu tare da daukar nauyin wurin kwana da abincinsu, amma yanzu N1,500 ma ba sa samu, Royal Times ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Wasu kuwa sun bayyana cewa, lokaci ma ya yi da za su daina wannan kazamar sana'a, inda suka yi tunanin kama wata harkar don iya rike kansu.

Sai tari, karuwai kan koka da cewa, sun shiga kazamar harkar ne don rike kansu duba da matsin rayuwa da suke ciki.

Karuwai sun yi yajin aiki

A Nairobi kuwa ta kasar Kenya, karuwan yankin Mombasa na kasar Kenya sun hada kai da sauran 'yan kasar Afrika ta gabas wajen yin bore game da yadda ake cin zarafinsu da direbobi.

An kama kimanin wadanda ake zargi guda 16 da fashi gami da yi wa wata mata ma'aikaciyar harkokin kasar waje fyade a kan titin daji, inda aka tsare su na tsawon kwana 15 don bai wa masu bincike damar kammala bincike, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

An kama wadanda ake zargin, bayan yawon da bidiyon yadda aka kai hari ga mai korafin yayi a 4 ga watan Maris. Inda aka samu labarin yadda jakadiyar kasar Zimbabwean ta kai kara kofishin yan sanda na Parklands.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.