Kasuwar Canji: Shugaban kasa Ya Zauna da Gwamnan CBN Game da Tsinkewar Dala

Kasuwar Canji: Shugaban kasa Ya Zauna da Gwamnan CBN Game da Tsinkewar Dala

  • Bola Ahmed Tinubu ya gaji da yadda Naira ta ke tangal-tangal, ya kira Gwamnan bankin CBN
  • A karshen taron da aka yi a Aso Rock, Folashodun Sonubi ya shaidawa ‘yan jarida yadda ta kaya
  • Gwamnan rikon kwaryan na CBN ya ce za a fito da hanyoyin da Dala za ta rage tsada a kasuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A sakamakon yadda Dalar Amurka ta ke tashi babu kaukautawa a kasuwar canji, Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da gwamnan bankin CBN.

Premium Times ta rahoto cewa Folashodun Sonubi wanda shi ne gwamman CBN na rikon kwarya, ya hadu da Shugaban kasa a fadar Aso Rock Villa a jiya.

Bayan zaman da ya yi da Bola Ahmed Tinubu, Mista Folashodun Sonubi ya zanta da manema labarai, inda ya yi magana kan tashin kudin kasar wajen.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN ya ce za dauki mataki a kan Dala Hoto; @Cenbank
Asali: Twitter

Dama can Shonubi ya na ganin yawan tashin da Dala ta ke yi ba na gaskiya ba ne, yake cewa hasashen mutane ya jawo hakan ba ainihin tsarin tattali ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Za a fito da wasu tsare-tsare a CBN

Gwamnan rikon kwaryan ya ce a karshen ganawarsa da Mai girma shugaban kasa, sun amince a fito da hanyoyin da za su haddasa karyewar kudin wajen.

A makon jiya ne aka ji yadda Bola Tinubu ya kafa tarihin da ba zai so ba, a karkashin gwamnatinsa aka samu ranar da aka saida Dalar Amurka a kan N950.

Meya jawo Dala ta ke tashi?

"Ba mu yarda cewa canjin da ake samu a kasuwar canji a dalilin zallar bukatun tattalin arziki ba ne, akwai dar-dar na bukata daga wajen mutane.

Kara karanta wannan

Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Ambato Kuskuren Da Shugaba Tinubu Ya Fara Daga Hawa Mulki

Wasu cikin dabaru da tsare-tsaren wanda ba zan iya fada maku ba, za su yi sanadiyyar da masu jita-jitar za su yi asara idan ba su bi sannu ba."

- Folashodun Sonubi

Tribune ta rahoto Gwamnan ya na mai bayanin yadda halin da ake ciki yake damun shugaba Tinubu.

Saboda haka ne babban bankin na CBN zai maida hankali wajen ganin an samu karin Dala har kasuwar canji domin talaka ya ji dadin tattalin arziki.

Yajin aikin 'Yan kwadago

A baya, an ji labarin yadda karyewar Naira a kasuwa ya jawo ‘yan kasuwa su ke ganin fetur zai tashi, lamarin da kungiyar NLC ba za ta yarda shi ba.

Shugaban kungiyar 'yan kwadago na kasa watau Kwamred Joe Ajaero ya nuna barazanar zuwa kotu sam ba za ta yi aiki a kan ma'aikata a yanzu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel