NLC: Idan Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki
- Ma’aikatan Najeriya ba za su yi na’am da karin farashin litar man fetur da ake tunanin za ayi ba
- Kungiyar NLC da TUC sun nuna babu abin da zai hana ayi yajin-aiki idan kudin fetur ya sake tashi
- Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero ya soki tsare-tsaren gwamnati, ya ce ana wahalar da ma’aikata
Abuja - Kungiyar NLC ta ‘yan kwadagon Najeriya ta na barazanar rufe ko ina da yajin aiki muddin aka ji farashin man fetur ya sake wani sabon tashi.
Rahotanni daga This Day sun tabbatar da cewa shugaban kungiyar NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero ya nuna ba za su lamunci karin farashi ba.
A yayin da ake jin cewa litar fetur za ta iya haura N720, kungiyar TUC ta ‘yan kasuwa ta nuna ta na goyon bayan duk matsayar takwararta, NLC.
Cif Chinedu Ukadike ya nuna tashin da dalar Amurka ta ke yi zai jawo fetur ya kara tsada. ‘Yan kasuwa su na sayen dala ne a kan N910 har zuwa N950.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba za ta sabu ba - Shugaban NLC
Da aka je taron kungiyar ‘yan kasuwar Afrika a garin Abuja, Joe Ajaero ya gargadi hukumomi da su guji yin abin da zai zama raina bukatun kungiyoyin.
Ganin yadda abubuwa su ke ta kara kamari, shugaban kungiyar ma’aikatan Najeriyan ya ce dole gwamnati ta soke tsare-tsaren da ke wahalar da jama’a.
A cewar Ajaero, manufofin gwamnati mai-ci ya yi sanadiyyar da albashi ya zama daidai da babu.
"Yanzu haka da mu ke nan, sun fara tunanin kara farashin kayan mai. Amma sai Ministan shari’a ya tafi kotu, ya samu izinin hana ‘yan kwadago yin komai.
Bari in fadi wannan, ba za mu bada sanarwar komai ba idan ba mu magance matsalar kare-kare biyu da aka yi na farashi ba, sai dai mu farka a ji karin kudi."
- Joe Ajaero
Masu harkar dizil sun koka
Duk a ranar ne kuma Daily Trust ta ce kungiyar NOGASA ta masu shigo da mai da gas ta yi kira da a cire harajin 7.5% da aka daura a kan man dizil.
‘Yan kungiyar ta NOGASA sun ce wannan haraji da gwamnatii ta ke karba ya kawo karin tsada, sannan an bukaci a magance matsalar tashin Dala.
$1 ta kama hanyar N1000
Farashin fetur zai kuma lulawa a gidajen mai saboda tashin Dala. An ji labari cewa ana bukatar $25m-$30m domin shigo da fetur daga kasar waje.
Dillalai sun nuna shigo da fetur ya zama aiki, wasu sun fara hakura saboda tsabagen tashin da Dala ta ke yi bayan Bola Tinubu ya karbi mulkin kasar.
Asali: Legit.ng