Lauyoyin Murja Sun Yi Fatali da Ita, Sun Fadi Nadamar da Suka Yi a Shari'arta

Lauyoyin Murja Sun Yi Fatali da Ita, Sun Fadi Nadamar da Suka Yi a Shari'arta

  • Yayin da aka gindaya sharuda kan ƴar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya, lauyoyinta sun nuna damuwa kan saɓa umarnin kotu da tayi
  • A U Hajji, shi ne jagoran lauyoyin Murja, ya ce sun yi nadamar tsaya mata duk da kalubalen da suka fuskanta a shari'ar da ake yi
  • Hakan ya biyo bayan saba umarnin kotu kan haramta mata ta'ammali da shafukan sada zumunta da matashiyar ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Lauyoyin da ke kare matashiya ƴar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya sun nuna damuwa kan yadda ta bijirewa umarnin kotu.

Jagoran lauyoyin, A U Hajji da aka fi sani da Abu Sajjan ya ce sun yi nadamar tsayawa Murja a gaban kotu saboda dabi'unta.

Kara karanta wannan

CNG: Manyan matakai 3 da Tinubu ya dauka na janye Najeriya daga dogara da man fetur

Yar Tiktok, Murja Kunya ta sake shiga sabuwar matsala
Lauyoyin Murja Ibrahim sun nuna damuwa kan yadda ta sabawa umarnin kotu. Hoto: Murja Ibrahim Kunya.
Asali: Facebook

Lauyan Murja ya ce sun yi nadama

Abu Sajjan ya ce ba su taba shiga kalubale kan wata shari'a ba tun da suke aiki sai a kan Murja kamar yadda Freedom Radio ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin takaici ne yadda muka dauki dukkan kalubale wanda ba mu taba yi ba a shekarun da muka yi muna aikin lauya."
"Abin bakin ciki ne kuma mun yi nadama sosai kan wannan lamari, ya kamata abi umarnin kotu."

- Abu Sajjan

Murja Kunya ta fitar da sabuwar waka

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta haramtawa Murna ta'ammali da kafafen sadarwa bisa sharadin belin da aka bata.

Sai dai Murja Kunya ta yi fatali da umarnin inda ta kuma fitar da wata sabuwar waka da take habaici a cikinta.

Umarnin da kotu ta ba Murja Kunya

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya yi martani kan matsalar da ya ke fuskanta daga haɗewar Atiku da Obi

Kakakin babbar kotun jihar, Babajibe Ibrahim ya tabbatar da cewa tuni suka ba da umarni sake cafke ta domin fuskantar hukunci.

Ya ce tun farko daman sun ba kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano umarnin kamo ta idan ta saba dokokin da aka gindaya mata.

Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da samun umarnin inda ya ce za su dauki matakin gaba.

Yadda kotu ta ba da belin Murja

A wani labarin, an ji yadda wata babbar Kotu a jihar Kano ta ba matashiyar 'yar TikTok, Murja Kunya beli kan kudi N500,000.

Kotun ta ba da belin ne da sharadin kawo mutum biyu da za su tsaya mata wanda daya daga ciki dole zai kasance na kusa da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel