Abin Da Mu Ka Fadawa Tinubu a Kan Shiga Yaki Da Nijar, Sheikh Kabir Gombe

Abin Da Mu Ka Fadawa Tinubu a Kan Shiga Yaki Da Nijar, Sheikh Kabir Gombe

  • Sakataren JIBWIS, Kabiru Haruna Gombe ya ce sun zauna da Bola Tinubu a kan rikicin Nijar
  • Malaman addinin Musuluncin sun fadakar da shugaban Najeriya kan hadarin yaki da makwabta
  • Da aka zo Jamhuriyyar Nijar, an ga haske wajen shawo kan sabanin shugabanci bayan juyin mulki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kabiru Haruna Gombe ya yi magana game da zaman da malaman musuluncin Najeriya su ka yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A rahoton da Aminiya ta fitar a safiyar Lahadi, an ji Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya ce sun ankarar da Bola Ahmed Tinubu game da illar yakar Nijar.

Kungiyar ECOWAS ta nuna za ta dauki duk wani mataki har da na bindiga kan makwabtan saboda Abdulrahmane Tchiani sun yi juyin mulki.

Tinubu Sheikh Kabir Gombe
Malaman addini da Bola Tinubu Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Jawabin Farfesa Salisu Shehu

Kara karanta wannan

Abun da Muka Tattauna Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar, Malaman Najeriya

Malamin Musuluncin yake cewa da su ka zanta da shugaban Najeriya, Farfesa Salisu Shehu ya yi bayani a kan tasirin yin amfani da karfin tuwo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da malaman su ka zauna da Abdulrahmane Tchiani wanda ya hambarar da Mohammed Bazoum a Nijar, sun bayyana masa matsayinsu.

Gar da gar, shugaban Jami’ar nan ta Al-Istiqamah da ke Sumaila a Jihar Kano ya yi gargadi a kan shiga yaki domin a dawo da mulkin farar hula.

Za a sake gayyato malamai a taron ECOWAS

Rahoton ya kara da cewa Kabir Gombe ya ce Bola Tinubu ya saurare su, kuma ya ce idan kungiyar ECOWAS za ta sake zama, za a gayyato Farfesan.

A cewar malamin, ko da lokacin Salisu Shehu ya kare, Mai girma Tinubu ya kara masa lokaci, hakan ya nuna ya damu da bayanin da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ga haske

Legit.ng Hausa ta ji Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi wa manema labarai jawabi kan makasudin zuwansu kasar makwabtan domin a samu yin sulhu.

Abdullahi Bala Lau ya ce sun samu kyakkyawar tarba daga sabon Fira Ministan kasar wajen, kuma sun gana da jami’an sabuwar gwamnatin sojan.

Tawagar ta hada da Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, Ibrahim Dahiru Bauchi, Mansur Sokoto, Nasir Abdulmuhyi, Yakubu Musa da Khalid Abubakar.

Sojojin ECOWAS sun fara harama

A karshen makon nan ne rahoto ya zo cewa an ɗaga taron manyan hafsoshin tsaron ECOWAS a kan juyin mulkin da sojoji su ka yi a Jamhuriyyar Nijar.

Tun farko an shirya taron ne domin samo hanyar da za a yi amfani da sojojin kasashen ECOWAS a Nijar. Tuni dakarun su ka kasance a shirin yaƙi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel