Malaman Najeriya Sun Yi Magana Bayan Sun Hadu da Sojojin da Su Ka Yi Juyin Mulki a Nijar

Malaman Najeriya Sun Yi Magana Bayan Sun Hadu da Sojojin da Su Ka Yi Juyin Mulki a Nijar

  • Tawagar malaman Najeriya da suka tafi Jamhuriyar Nijar a kokarinsu da neman maslaha tsakanin sojojin juyin mulki da ECOWAS ta gana da shugabannin sojin Nijar
  • Kamar yadda jagoran tafiyar Mallam Bala Lau ya bayyana, sun samu nasara a kan abun da ya kai su
  • Bala Lau ya ce sojojin Nijar a shirye suke su tattauna da wakilan kungiyar ECOWAS a yanzu kuma a koda yaushe

Jamhuriyar Nijar - Malaman addinin Musulunci a Najeriya sun samu damar zantawa da sojojin juyin mulki a Janhuriyar Nijar yayin da ake ci gaba da takkadama tsakaninsu da kungiyar ECOWAS.

Malaman Najeriya sun ajiye banbancin akida sun hada kai zuwa Nijar a kokarin da suke na ganin an samu maslaha tare da hana zubar jini a kasar ta yammacin Afrika.

Malaman Najeriya sun tattauna da sojojin juyin mulkin Nijar
Malaman Najeriya Sun Yi Magana Bayan Sun Hadu da Sojojin da Su Ka Yi Juyin Mulki a Nijar Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Kamar yadda sashin Hausa na BBC ra haoto, Malaman karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar Izallah ta Najeriya, sun zauna da sojojin juyin mulki na tsawon sa'o'i uku.

Kara karanta wannan

Yaki Da Nijar: Abin Da Malamai SuKa Fadawa Bola Tinubu, Sheikh Kabir Gombe

Sojojin Nijar sun nemi afuwar kin sauraron tawagar Sarkin Musulmi, Bala Lau

Jagoran tafiyar, Sheikh Bala Lau ya sanar da BBC cewar sojojin sun fara da neman afuwa a kan kin sauraren tawagar tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala Lau ya ce:

"Datse wutar lantarki da hana shiga da abinci Jamhuriyar Nijar ya haddasa zanga-zanga kuma matasa sun fito a wannan ranar, sojojin sun ce tsoron kada a yi masu rashin da'a shine ya sa ba su ba su damar zama da su ba, amma dai sun nemi mu ba da hakuri a madadinsu."

Sojojin juyin mulkin Nijar sun ba da damar tattaunawa da ECOWAS

Dangane da inda aka kwana, Shehin malamin ya ce an samu kofar tattaunawar diflomasiyya, a cewarsa, sojojin sun ce a shirye suke yanzu su tattauna da wakilan kungiyar ECOWAS a kowani lokaci.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Majalisar ECOWAS ta dare kan lamarin Nijar, bayanai sun bayyana

Ya ci gaba da cewa:

"Tun daga yadda suka karɓe mu muka san cewa tafiyarmu ta yi nasara. Sun turo ministoci da Firaiministan ƙasar filin jirgin sama domin su zo su tare mu, sun kai mu kuma har fadar shugaban ƙasa da kansu.
"Daga irin tarbar da suka yi mana muka san cewar hakarmu ta cimma ruwa. Sun aiko ministoci da firaiministan kasar zuwa filin jirgin sama domin su tarbe mu, da kansu suka kai mu har fadar shugaban kasar.
"Mun shafe kusan tsawon sa'o'i uku muna tattaunawa kan batutuwa da dama. Mun isar da sako kuma mun yi masu nasiha domin hana zubar jini, don idan an san farkon rikici ba a san karshensa ba."

Har ila yau, malamin ya ce sojojin na Nijar sun yi farin ciki tare da murna kan wannan kokari sannan sun nuna za su ba da hadin kai domin a samu a zauna.

Sannan ya kuma ce akwai wasu sakonni da dama da za su isar zuwa ga shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wadanda ba su fade shi ba a waya.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Da aka tambaye shi kan lokacin da sojojin suke ganin ya kamata a zauna da su, malamin ya ce:

"A ko ina aka kira su za su je kuma da kowani lokaci."

Majalisar ECOWAS ta kira taron gaggawa

A baya mun kawo cewa ana tsaka da fama da lamarin karbe mulki da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, majalisar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), za ta gudanar da wani taro na musamman.

An tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel