Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa

Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa

- Rsohuwar Ministar kudi a Najeriya, da yiyuwar ta kasance sabuwar Darakta-Janar na WTO

- Hukumar ta sanar da sabon nadin Darakta-Janar din zai gudana ranar 15 ga watan Fabrairu

- A baya, an bayyana tsohuwar ministar a matsayin 'yar takara tilo da ta fito neman kujerar

Babban Kwamitin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, WTO, ya ce zai duba yiwuwar nada Darakta-Janar na gaba mako mai zuwa ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito

Ku tuna cewa tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, ita ce 'yar takara tilo da ta bayyana a wannan matsayi, biyo bayan sauka daga wani dan takarar wanda ya kasance Minista a Koriya a makon da ya gabata.

KU KARANTA: Ku shirya jure tsadar man fetur, Ministan mai ga 'yan Najeriya

Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa
Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa Hoto: CNN
Asali: UGC

Kungiyar, a cikin wata sanarwa mai taken, ‘WTO General Council da za ta yi la’akari da nadin Darakta-Janar na gaba’ da ta wallafa a shafinta na intanet a ranar Talata, ta ce za a gudanar da taro na musamman na Babban Kwamishinanta a ranar 15 ga Fabrairu.

“Babban Kwamitin WTO zai yi taro na musamman a ranar 15 ga Fabrairu da misalin karfe 3:00 na yamma lokacin Geneva don yin la’akari da nadin Darakta-Janar na gaba. Taron zai gudana ne cikin tsari na kamala,” sanarwar ta kara da cewa.

KU KARANTA: Ku shirya jure tsadar man fetur, Ministan mai ga 'yan Najeriya

A wani labarin, Kungiyar kasuwancin duniya WTO ta amince da tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala matsayin daya daga cikin yan takaran kujerar shugabancin kungiyar, The Cable ta ruwaito.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo inda tace: "Kasar Najeriya a ranar 9 ga Yuni 2020 ta zabi Dr Ngozi Okonjo Iweala matsayin wacce za tayi takarar kujeran shugaban WTO domin maye gurbin shugaban na yanzu, Mr Roberto Azevedo, wanda ya sanar da cewa zai sauka a ranar 31 ga Agusta, 2020."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel