Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

  • Wasu sun taso Malam Nasir El-Rufai a gaba saboda ganin za a ba shi Minista a gwamnatin tarayya
  • Ana tunawa tsohon Gwamnan abin da ya fada game da rike mukamin, ana zargin ya lashe amansa
  • Amma an gano bidiyo a Twitter inda Bola Tinubu da kan shi ya roki El-Rufai ya yi aiki da gwamnatinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Nasir El-Rufai yana shan suka saboda an zabo shi cikin wadanda ake niyyar nadawa a matsayin Ministocin gwamnatin tarayya.

Legit.ng Hausa ta lura ana amfani da kalaman tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna da ya rika nuna bai bukatar rike mukamin Minista a kasar.

A wasu lokutan, Malam Nasir El-Rufai ya ce shekaru sun ci masa, saboda haka yana bukatar ya hakura da rike kujerar gwamnati a Najeriya.

Tinubu El-Rufai Ministoci
Bola Tinubu ya zabi Nasir El-Rufai cikin Ministoci Hoto: thenewsguru.com
Asali: UGC

Sannan akwai inda ‘dan siyasar yake cewa ya shaidawa Bola Tinubu bai bukatar wata kujera.

Kara karanta wannan

Malaman Addinin Musulunci a Arewa Sun Roki a Hana El-Rufai Yin Minista, Sun Bayyana Dalili

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jahili yake maimaita aji"

Amma sai ga shi Malam El-Rufai ya kama hanyar sake zama Ministan tarayya a shekara 63, matsayin da ya rike tsakanin 2003 da 2007.

Ana haka sai ga wani bidiyo inda aka ji Shugaba Bola Tinubu a lokacin yana neman takara, ya fito yana rokon Malam El-Rufai ya yi aiki da shi.

Kar ka gudu wannan karon

Yayin da Tinubu ya ziyarci garin Kaduna a sa’ilin kamfe, ya lallabi Gwamnan ya yi masa alkawarin ba zai bar Najeriya, ba, zai yi aiki tare da shi.

A karshe sai da tsohon Ministan na birnin tarayya Abuja ya fada da bakinsa a dakin taron na Shehu Musa ‘Yaradua cewa zai karbi tayin mukami.

Tinubu ya kafe yana cewa ba zai bar dandamalin ba har sai ‘dan siyasar ya amsa, dolen sa ya ce zai yi aiki da gwamnatin Tinubu idan an ci zabe.

Kara karanta wannan

Ganduje da Tsofaffin Gwamnoni 7 da Tinubu Ya Watsar Wajen Rabon Mukaman Minista

Alfarmar da Tinubu ya nema

"‘Danuwa na Nasir (El-Rufai), yi alkawari ba za mu bar ka, ka tsere daga kasar nan ba, ta haka ne kurum zan sauka daga kan mimbarin nan.
Sai ka dauki alkawari."

- Bola Tinubu

El-Rufai ya yi alkawari

Har sun tafi sai aka ji Gwamnan ya sake dawowa, ya dauki wannan alkawari a gaban dinbin jama’a.

“Nayi alkawari”
“Nayi alkawari ko da na ba cikakken lokaci ba ne.”

- Nasir El-Rufai

Hasashen ragowar Ministoci

A hasashenmu, kun ji ‘Dan takaran Shugabancin kasa a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai iya samun kujera a FEC a jeri na biyu da za a fitar.

‘Yan siyasa da-dama da su ka sha kashi a hannun PDP za su iya shiga sahun Ministocin, akwai tsofaffin Gwamnonin Legas da watakila su shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel