Masu Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Matakin EU Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa a Jamhuriyar Nijar

Masu Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Matakin EU Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa a Jamhuriyar Nijar

  • Yanzu muke samun labarin yadda aka farmaki ofishin jakadancin Faransa a jamhuriyar Nijar
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan sanar da yin juyin mulki a kasar da ke makwabtaka da Najeriya
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da cece-kuce kan abin da ya faru a Nijar, masu sharhi na ci gaba da jawabi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar - A wani yanayi mai ban mamaki, wasu masu zanga-zanga sun farmaki ofishin jakadancin Faransa a Jamhuriyar Nijar, RFI Hausa ta ruwaito.

A baya an ruwaito yadda Amadou Abdramane, wani Kanal din soja da ya sanar da tsige shugaban farar hular dimokradiyya Mohamed Bazoum daga mulki a wani jawabi da ya yi cikin daren Laraba.

Abdramane ya rusa kundin tsarin mulkin kasar, inda ya dakatar da dukkan hukumomi tare da rufe iyakokin kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Akwai sharrin Turawa: Shehu Sani ya fadi abubuwa 5 da suke sa juyin mulki a Afrika

An farmaki ofishin jakadancin Faransa a Nijar
Yadda aka kai farmaki ofishin jakadancin Faransa | Hoto: @TheCable
Asali: Twitter

Yadda zanga-zanga ta barke

A wani abin da ya yi kama zanga-zangar adawa da tsoma bakin gwamnatin Faransa a lamurran Nijar, magoya bayan gwamnatin mulkin soji sun yi gangami a kan titunan birnin Yamai babban birnin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ga suna daga tutocin kasar Rasha tare da ambatan sunan Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha, tare da yin tir da Allah wadai da tsohuwar mai mulkin mallakar Nijar, Faransa.

Abin da yake faruwa a Nijar yanzu haka, kasar Faransa ta janye dukkan tallafin da take tura wa kasar sanadiyyar juyin mulkin, rahoton TheCable.

Martanin Turawa

A ranar Asabar ne babban wakilin kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce kungiyar EU ba ta amince da juyin mulkin Nijar ba, kuma ba za ta amince da hukumomin da suka yi sanadiyar juyin mulkin ba.

Ya ce Bazoum, shugaban da ya rasa kujerarsa a yanzu, an zabe shi ne ta hanyar kada kuri’un dimokuradiyya kuma ya kasance shugaban kasar Nijar sahihi kuma na halas.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tashin Hankali a Nijar Yayin da Abdourahmane Tchiani Ya Ayyana Kansa a Matsayin Sabon Shugaban Kasar

A halin yanzu, shugabannin kasashe Afrika na ECOWAS suna ganawa da shugaba Bola Tinubu, wanda shi ne sabon shugaban ECOWAS kan lamarin na Nijar.

Damu dangane da lafiyar Bazoum, Buhari ya yi bayani kan juyin mulkin Nijar

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaban kasar Nijar Mohammed Bazoum.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne ranar Juma'a ta shafinsa na Twitter.

Buhari ya ce ya yi matukar girgiza da yadda abubuwa suka kasance a jamhuriyar Nijar kamar yadda jama'a da dama suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.