Tallafin Fetur: Da Ya Sha Suka, Tinubu Ya Janye Tsarin da Ya Yi Niyyar Fito da Shi

Tallafin Fetur: Da Ya Sha Suka, Tinubu Ya Janye Tsarin da Ya Yi Niyyar Fito da Shi

  • Bola Ahmed Tinubu ya ji koke-koke da korafin jama’a a kan rabawa talakawa kyautar N8, 000 a wata
  • Shugaban kasar ya bada umarnin dakatar da tsarin domin a sake yin nazari saboda sukar da ya sha
  • Dele Alake ya shaida cewa Gwamnatin Tinubu ta san halin da ake ciki, za a raba taki da kayan abinci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja – Mai girma Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin gaggauta sake duba tsarin da ya yi niyyar kawowa domin a rage radadin janye tallafin man fetur.

A wani jawabi da ya fito daga ofishin Dele Alake a yammacin Talata, Shugaban Najeriya ya shaida ya janye tsarin sakamakon rashin karbuwa da ya yi.

Mai taimakawa wajen harkoki na musamman, sadarwa da dabaru ya ce Bola Ahmed Tinubu ya yi hakan ne domin ya yi alkawarin zai rika sauraron jama’a.

Kara karanta wannan

Duniya Kenan: Tsohon Jigo Ya Tuno ‘Rigimarsa’ da Shugaban APC da Ya Sauka

Tinubu
Shugaban Najeriya ya cire tallafin fetur Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jama'a ba su yi na'am da tsarin ba

Tun farko, hadimin ya ce gwamnatin Tinubu ta yi niyyar kawo tsarin ne domin farfado tattalin arziki da kawo sa’ida, amma mutane su ka yi tir da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga gidajen talakawa tubus har miliyan 12 da aka so su ci moriyar N8, 000 a wata, Mista Alake ya ce akwai wasu tsare-tsaren da gwamnati take da shi.

Jawabin ya ce shugaban kasar ya kuma bada umarnin raba takin zamani da hatsi ga manoma da gidaje miliyan 50 da ke fadin Najeriya domin sun amfana.

Alake yake cewa za a raba wadannan kaya ne domin rage radadin da al’umma su ke ciki a yau.

A jawabinsa, The Nation ta ce Mai ba shugaba Tinubu shawaran ya sake jaddada cewa ya zama dole ne gwamnatin tarayya ta kawo karshen tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Masoyin Tinubu Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, Ya Yi Iƙirarin Daukar Mummunan Mataki

Yayin da aka janye wannan mugun tsari a cewarsa, wajibi ne a samar da tsare-tsaren kawo tallafi.

Jawabin Dele Alake

"A matsayinsa na jagora mai sauraron jama’a wanda ya sha alwashin tausayawa ‘Yan Najeriya da manufofi da tsare-tsarensa, shugaban kasa ya bada umarnin nan:
1. A sake duba tsarin raba kyautar N8, 000 domin kawo sa’ida ga marasa karfi ba tare da bata lokaci ba.
2. A sanar da mutanen Najeriya daukacin tsarin tallafin da gwamnati ta ke da shi.
3. A fito da taki da hatsi ga kimanin manoma da gidaje miliyan 50 da ke jihohi 36 da birnin tarayya.

- Dele Alake

A rabu da fetur, a komawa gas

Bola Tinubu yana so Gwamnatin Najeriya ta ci moriyar gas domin samar da cigaba kamar yadda aka ji mai ba shi shawara ta na fada a wani rahoto.

A lokacin da man fetur yake tsada, sabuwar Gwamnati ta na kokarin kawo mafita. An kafa Sakatariyar gas a Abuja a karkashin jagorancin Ed Ebong.

Asali: Legit.ng

Online view pixel