Uwar Sarki ta Kai Shi Kotu, Ta Roki Alkali Ya Sake Duba Rabon Gadon Mai Martaba

Uwar Sarki ta Kai Shi Kotu, Ta Roki Alkali Ya Sake Duba Rabon Gadon Mai Martaba

  • Asiya Nuhu Sanusi, tayi karar Sarki mai-ci a Dutse, Hamim Nuhu Sanusi, a kotun daukaka shari’a
  • Matar tsohon Sarki da wasu mutum bakwai, suna kalubalantar Sarkin Dutse, Hamim Nuhu Sanusi
  • Ana tuhumar Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da yin kuskure a rabon gadon iyalan mamacin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jigawa - Daya daga cikin matan tsohon Sarkin Dutse, Asiya Nuhu Sanusi tayi karar Mai martaba Sarki, Hamim Nuhu Sanusi a wata kotun shari’a.

A ranar Litinin, Aminiya ta kawo labari cewa Hajiya Asiya Nuhu Sanusi ta na neman hakkin ta a gadon tsohon Sarki, Marigayi Alhaji Nuhu Sanusi.

Wani Lauya mai suna Abdulhali Ali Esq ya shigar da kara a madadin mai dakin tsohon Sarkin, tana mai tuhumar mutane bakwai gaban Alkali.

Sarkin Dutse
Mai martaba Sarkin Dutse, Marigayi Muhammad Nuhu Sanusi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kotun shari'a tayi kuskure

Abdulhali Ali Esq ya kalubalanci hukuncin babban kotun shari’a da Khadi Ado Birnin Kudu ya zartar, ya ce an yi kuskure a karar da aka kai masa.

Kara karanta wannan

Kwanaki Kadan da Yin Juyin Mulki a Nijar, Bola Tinubu Ya Tafi Biki a Kasar Afrika

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar marigayin ta na so Alkalin babban kotun daukaka kara na shari’a ya raba gardama, ya fadi ko Mai shari’a Ado Birnin Kudu ya yi kuskure.

Kotun daukaka karara za ta yanke hukunci ko dangi za su iya karbe dukiya mai lamba 17 JGNL/DU/RES/94/264, a maida su cikin sauran gado.

Solacebase ta ce Asiya Nuhu Sanusi ta na ikirarin Marigayi ya mallaka mata dukiyar da yake raye.

A karar mai lamba SCAJG/CV/2023, za a ji ko wasikar tsohon Sarki mai lamba LPR/DU/3 da satifiket JGNL/DU/RES/94/511 ba su gamsar ba.

Mai karar ta ce an bar wa kishiyarta mai suna Hajiya Gaji Nuhu Sanusi wata dukiya mai lamba JGNL/DU/RES/92/5, amma shari’a ta canza a kan ta.

A cewar matar marigayin, Mai martaban ba zai taba yin rashin adalci ga matansa ba don haka ya rabawa matansa gidaje biyu a lokacin yana da rai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Yi Magana Kan Hoton Sanusi II Da Ya Dawo Gidan Gwamnati

Lauyan ya kafa hujjoji da sashe na 36 (1) na kundin tsarin mulki da wasu ayoyi a kan rabon gado da wasiyya. Har yanzu ba a sa ranar fara zama ba.

Hoton tsohon Sarki a Gidan Gwamnatin Kano

An ji labari Hadimin gwamnan Kano ya ce matukar ana so a girmama tarihi dole a saka hoton Muhammadu Sanusi II a dakin taron gidan gwamnati.

Ganin ana ta surutu, Salisu Hotoro ya fitar da jawabi cewa ganin hoton Sunusi II a fada bai kamata ya zama sabon wani darasi na tattaunawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel