CBN Ya Bude Asusun Mutane da Kamfanoni 440 da Aka Rufe da Aka yi Canjin Gwamnati

CBN Ya Bude Asusun Mutane da Kamfanoni 440 da Aka Rufe da Aka yi Canjin Gwamnati

  • A makon nan ne aka ji sanarwa daga Babban bankin Najeriya game da bude akawun da aka rufe
  • Shekaru biyu da su ka wuce, aka hana ficewar kudi daga banki a asusun wasu kamfanoni da mutane
  • Za a janye takunkumin, ana sa ran kudi zai iya fita daga akawun din daidaiku da kuma ‘yan kasuwan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN ya umarci bankuna su cire takunkumin da ke kan wasu asusu 400 da kamfanoni da daidaiku su ka mallaka.

The Cable ta ce kafin yanzu, bankunan sun hana a iya fita da kudi daga wadannan akawun.

Idan aka kakaba irin wannan takunkumi, kudi ba za su fita daga asusun ta hanyar amfani da katin ATM, takardar cheques, POS ko makamancinsa ba.

Bankin CBN
Bankin CBN ya ce a bude asusu 440 Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

Sanarwar da CBN ya fitar

Kara karanta wannan

CBN Ya Yi Karin Haske Kan Makomar N200, N500 Da N1000 Da Aka Kori Emefiele

Tashar Arise ta ce A.M. Barau ya fitar da sanarwa a wata takarda da ta fito a ranar Talata a madadin Darektan da yake sa ido kan harkokin bankuna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta ce bayan bude wadannan asusu domin cigaba da mu’amalar fitar da kudi, an umarci bankunan su sanar da wadanda su ka mallaki asusun.

Rahoto ya ce kamfanonin da abin ya shafa sun hada da: Bamboo Systems Technology Ltd, Escale Oil & Gas Limited da Rise Vest Technologies Ltd.

Haka zalika abin ya shafi kamfanin Chaka Technologies Limited, har da abokiFX Ltd, Nairabet International sai kamfanin Northwood Energy Services.

Nairametrics ta ce umarnin ya ba kamfanin Crypto na Yellow Card Financial da Proport Marine Limited da wasunsu damar cire kudinsu a banki.

Sauran kamfanonin da su ka tsira

Kara karanta wannan

Bidiyon Rashin Da’a Ga Musulunci: MURIC Ta Caccaki Davido, Ta Bukaci DSS Da Ta Gayyaci Mawakin

A lokacin da CBN ya ba bankuna umarni a hana fitar kudin kamfanonin, matakin ya shafi daga Bakori Mega Services zuwa Ashambrakh General Enterprise.

Ragowar kamfanonin su ne: Namuduka Ventures Ltd, Crosslinks Capital & Investment Ltd, IGP Global Synergy Ltd, Davedan Mille Investment Ltd.

Bayan Urban Laundry, akwai Advanced Multi-Links Services Limited, Spray Resources, Al-Ishaq Global Resources Limited, sai Himark Intertrades.

Akwai Charblecom Concept Limited, Wudatage Global Resources, Treynor Soft Ventures, Fyrstrym Global Concepts Limited, da Samarize Global Nigeria.

Ragowar kamfanin da ya cika jerin shi ne Zahraddeen Haruna Shahru. Duk abin da aka yi, bankin CBN bai fadi dalilin rufe ko bude duk akawun dinnan ba.

Rayuwa ta yi wahala a yau

Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari ya ce dole a kara albashi, an samu rahoto cewa malamin ya koka da yadda farashin man fetur ya gagari ma'aikata.

Shehin ya na ganin wajibi ne Hukumomi su gaggauta samarwa talakawa isassun motoci, domin ya ce zirga zirgansu da sauki, hakki ne ba alfarma ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel