Babban Basarake Mai Daraja Ta Daya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Jihar Nasarawa

Babban Basarake Mai Daraja Ta Daya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Jihar Nasarawa

  • Jihar Nasarawa ta yi rashin babban basarake, Alhaji Aliyu Daudu, wanda ya koma ga mahaliccinsa ranar Litinin
  • Dauda babban basarake ne mai daraja ta ɗaya a Gadabuke a yankin Gadabuke cikin ƙaramar hukumar Toto ta jihar Nasarawa
  • Alhaji Aliyu Abdullahi Tashas, shugaban ƙaramar hukumar Toto ya bayyana rasuwar basaraken a matsayin babban rashi ga al'ummar Gada

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Toto, Nasarawa - Alhaji Aliyu Daudu, babban basarake mai daraja ta ɗaya a Gadabuke cikin yankin Gadabuke na ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa ya riga mu gidan gaskiya.

Alhaji Aliyu Daudu ya gamu da ajalinsa ne inda ya bar duniya yana da shekara 96 ranar Litinin, 24 ga watan Yulin 2023.

Babban basarake a jihar Nasarawa ya rasu
Jihar Nasarawa ta yi rashin babban basarake Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

Wani daga cikin iyalan basaraken, Abdullahi Zakari, shi ne ya tabbatar da rasuwar marigayin ta wayar tarho ga manema labarai ranar Talata, 25 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Fitaccen Sanata Ya Yi Babban Rashi a Abuja

Babban basaraken ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya

Zakari ya ƙara da cewa basaraken ya rasu ne a babban asibitin gwamnatin tarayya dake Keffi ranar Litinin, 24 ga watan Yuli da daddare bayan ya daɗe yana fama da jinya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alhaji Aliyu Abdullahi Tashas, shugaban ƙaramar hukumar Toto, ya nuna alhininsa kan rasuwar basaraken mai shekara 96 a duniya.

Alhaji Aliyu ya bayyana cewa za a riƙa tunawa da marigayin bisa jajircewa da dattakon da ya nuna wajen ci gaban al'ummar Gada da gaba ɗaya ƙaramar hukumar Toto.

Jihar Nasarawa dai tana ɗaya daga cikin da su ke a yankin Arewa ta tsakiya inda jam'iyyar APC ke mulki.

Babban Limamin Suleja Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa babban limamin babban masallacin Juma'a na Suleja a jihar Neja ya koma ga mahaliccinsa cikin tsakar dare a gidansa dake garin na Suleja.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Hawaye Sun Ƙwaranya Bayan Babban Limami a Jihar Neja Ya Rasu Sa'o'i Kadan Bayan Ya Dawo Daga Saudiyya

Sheikh Shuaibun Dahiru ya yi bankwana da duniya ne bayan jim kaɗan bayan ya dawo gida Najeriya daga ƙasa mai tsarki bayan ya kammala gudanar da aikin Hajjin bana.

Babban limamin babban masallacin Juma'ar na Suleja wanda ya iso gida lafiga daga Saudiyya ya rasu ne a sakamakon bugun zuciya da ya same shi cikin dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel