Malamai Sun Fara Suka Kan Rufe Sheikh Dutsen-Tanshi Na Dogon Lokaci a Kurkuku

Malamai Sun Fara Suka Kan Rufe Sheikh Dutsen-Tanshi Na Dogon Lokaci a Kurkuku

  • Sheikh Tijjani Yusuf Guruntum ya fito yana neman hukuma tayi wa Abdulaziz Dutsen Tanshi adalci
  • Malamin addinin yana ta fama da dauri tun watan Mayu, Gurutum ya ba gwamnatin Bauchi shawara
  • Malamin ya ce idan dai babu siyasa a daure Dr. Dutsen Tanshi, to kyau a hada masa zama da malamai

Bauchi - Tijjani Yusuf Guruntum yana cikin malaman musulunci da ake sauraro a Najeriya da kasashen Afrika, ya soki rufe Dr. Abdulaziz Dutsen Tanshi.

A wani karatu da ya yi kwanan nan da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi, Sheikh Tijjani Yusuf Guruntum ya ce babu adalci a cigaba da tsare malamin addinin.

Malaman Musulunci
Malaman Musulunci, Tijjani Yusuf Guruntum da Abdulaziz Dutsen Tanshi Hoto: darulfikr.com/dailypost.ng
Asali: UGC

Daily Trust ta ce Kotu ta bada belin fitaccen malamin da sharadin zai kawo wani Hakimi mai digirin PhD da ‘dan kasuwa da za su tsaya masa a garin Bauchi.

Kara karanta wannan

An Rasa Inda Tattalin Arziki Ya Dosa, Za a Shafe Kusan Kwanaki 60 Babu Ministoci

Tsaurin sharudan belin da Mai shari’a Malam Hussaini Turaki ya bada, ya jawo har yanzu wannan malami yana gidan gyara hali, abin da wasu su ka fara suka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba gidan yari ne mafita ba

Guruntum ya ce abin da ya dace shi ne a bada damar a zauna da masu ja da Dr. Dutsen Tanshi, ya ce ko Firauna ya kyale Annabi Musa (AS) gasa da bokaye.

Shehin malamin yake cewa tun a zamanin baya idan aka samu wanda ya zo da wani bakon lamari a addini, ana hana shi ne da malaman addini su yi zama na ilmi.

Malam yana zaune a gidan yari, babu alkiblar shari’a. Menene dalili na wannan gidan yari da malam yake yi?
Idan mun dauka cewa wadancan bayanai da malam ya yi a tafsirin Ramadan ce ta kawo wannan matsalar, adalci shi ne a zaunar da shi da malamai.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

Ba maganar gidan yari ba ne, tun da magana ce da ta shafi addini, a hada shi da malamai.”

- Sheikh Tijjani Yusuf Guruntum

Ko akwai siyasa a lamarin?

Guruntum ya ce idan kuwa ba haka ba, akwai burbushin siyasa tare da cewa kowa ya yarda Dutsen Tanshi mutum ne mai kishin addini da al’ummarsa.

A cewar malamin, yadda Dutsen Tanshi ya yi wa Gwamnatin APC adawa a 2019, haka ya sake zama ‘dan hamayyar gwamnati mai-ci a zabe na 2023.

Guruntum ya tunawa Gwamnati mai-mulki irin gudumuwar da malamin ya ba su a 2019, shi ne salon da ya dauka wajen ganin an yi waje da ita a bana.

Bello Yabo ya yi magana

Sheikh Bello Yabo ya na cikin sahun masu sukar lamarin, ya ce abin da ya faru ya tabbatar da ba a dalilin karatun Dr. Dutsen Tanshi aka cafke shi ba.

A ra'ayin malamin na Sokoto, sabani tsakanin Bala Mohammed da malamin ne ya jawo aka rufe shi, ya na mai Allah-wadai da Gwamna na jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: Da Ya Sha Suka, Tinubu Ya Janye Tsarin da Ya Yi Niyyar Fito da Shi

"Zalunci ne" inji wani dalibi

Da mu ka yi magana da wani mai bibiyar karatun malamin a Bauchi, Shamsuddeen Ahmad Rufai ya fada mana babu adalci a matakin da aka dauka.

Shamusuddeen Rufai ya fadawa Legit.ng Hausa cewa ba a san asalin laifin da ake zargin malaminsu da aikatawa ba, illa kawai sukar gwamnati mai-ci.

Dalibin ya ce malamai sun sallama masa kan abin da ya fada game da neman ceto, ya ce rike Sheikh Dutsen Tanshi babu gaira babu dalili yana da hadari.

Muhammadu Buhari a Katsina

A wani rahoto, an ji cewa bayan dawowa daga Landan, Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Katsina domin halatar taro a Katsina daga mahaifarsa.

Dr. Dikko Umaru Radda ne mai masaukin baki a taron gidauniyar jihar Katsina. Wannan ne karon farko da tsohon shugaban kasar ya je wani taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel