An Rasa Inda Tattalin Arziki Ya Dosa, Za a Shafe Kusan Kwanaki 60 Babu Ministoci

An Rasa Inda Tattalin Arziki Ya Dosa, Za a Shafe Kusan Kwanaki 60 Babu Ministoci

  • Har yau Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai iya nada sababbin Ministocin da za su yi aiki da gwamnatinsa ba
  • Shugaban Najeriyan ya kawo wasu tsare-tsaren tattalin arziki da su ka jawo mutane su na wayyon Allah
  • A lokacin zabe, Tinubu ya yi alkawarin kawo sauki, a yanzu ana cewa sai a gaba za a ga tasirin manufofinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Za a dauki tsawon kusan watanni biyu ba tare da an yi zaman majalisar zartarwa a Najeriya ba domin an gagara nada sababbin Ministocin kasar.

Rahotanni daga irinsu Punch sun ce rashin gwamnati a kasa ya jawo an gagara gane inda sabuwar gwamnatin Najeriya ta sa gaba tun da ta shiga ofis a Mayu.

Bola Ahmed Tinubu wanda ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu bai zabi Ministocinsa ba har majalisar dattawa ta dage zama zuwa makon gobe.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: Da Ya Sha Suka, Tinubu Ya Janye Tsarin da Ya Yi Niyyar Fito da Shi

Tinubu
Tinubu da wasu shugabannin Afrika Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A doka, wajibi ne a gabatar da sunayen wadanda yake so Sanatoci su tantance a matsayin Ministoci cikin kwanaki 60, wa’adin zai kare a karshen Yuli.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsare-tsaren Bola Tinubu

Daga lokacin da Bola Tinubu ya karbi mulki, ya cire tallafin man fetur wanda hakan ya yi sanadiyyar karin tsadar abinci da sauran kayayyaki a kasuwanni.

A yau direbobi da-dama su na kukan cewa ciniki ya ragu masu saboda tashin kudin zirga-zirga. Wannan tsari ya shafi kanikawa, sun rage kasuwa a yau.

Wani direban Keke Napep ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa da kyar ya ke iya maida kudinsa a rana, haka abin yake ga ‘yan acaba da ke yin haya da babur.

An fara yunkurin rage haraji, amma Gwamnati ta kawo tsarin da ya jawo tashin kudin kasar waje. Mun tuntubi masani domin jin tasirin tsare-tsaren nan.

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

Ra'ayin masana tattalin arziki

Dr. Usman Adamu Bello masanin tattalin arzki ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya shaida mana cewa an sake cusa talaka cikin kangi da kunci.

Gwamnati ta ce an janye tallafin fetur ne domin ba talakawa yake amfana ba, Usman Bello yana ganin wannan ba gaskiya ba ne, shawarar manyan Duniya ce.

Tun da Najeriya ta na cikin manyan masu arzikin danyen mai, a cewarsa bai dace a ce talaka ba zai amfana ba, musamman a kasa mai fama da mugun talauci.

"Har a kasashe irin Amurka da aka cigaba, akwai tallafi na noma, kiwon lafiya da zaman banza."

- Dr. Usman Adamu Bello

A dawo da daukar aiki - Majalisa

An rahoto 'dan majalisar Delta, Hon. Francis Waive ya ce a halin da aka samu kai a ciki, dole a dawo a rage masu zaman kashe wando ta hanyar daukar aiki.

Muhammadu Buhari ya haramtawa kowa daukar aiki a gwamnatin tarayya a lokacin yana mulki sa'ilin da aka shiga wani matsin lambar tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel