Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

  • Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa Sanatoci takarda a game da nadin shugabannin hukumar NEDC
  • Majalisar Dattawa ta karbi sunayen Janar Paul Tarfa (rtd) da Mohammed Alkali, za a tantance su
  • An samu sabani kan wadanda za su rike NEDC da aka kafa domin mutanen Arewa maso gabas

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nemi izinin majalisar dattawa a nadin shugabanni da majalisar da za ta rika sa ido a aikin hukumar NEDC.

Rahoton Daily Trust ya ce shugaban kasar ya bada sunayen wadanda Muhammadu Buhari ya ki yarda ya kara masu wa’adi ne a lokacin shi yana ofis.

Tsohon shugaban kasa Buhari bai amince da wadannan shugabanni ba, hakan ya kai ga Ministar jin kai da bada agaji, ta nada wasu shugabanni dabam.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya aikawa Majalisa takarda Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

An yi waje da Umar Abu Hashidu

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Rasa, Tinubu Ya Yarda Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC

Legit.ng Hausa ta fahimci Sa’diya Farouk Umar ta zabi Umar Abubakar Hashidu a matsayin shugaban hukumar, amma bai samun yardar majalisa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mahaifin Umar Abubakar Hashidu ya yi Gwamna a Gombe tsakanin 1999 da 2003 a APP.

Rahoton ya ce sauran masu ruwa da tsaki daga Arewa maso gabas, a ciki har da Gwamnoni ba su yi na’am da mukaman ba, su ka ce ba a tuntube su ba.

Sai dai aka ji an dauke su a jirgi zuwa hedikwatar hukumar da ke Maiduguri domin fara aiki.

Janar Paul Tarfa ya dawo NEDC

A wasikar da Tinubu ya aikawa Sanatoci, Punch ta ce ya bukaci ayi amfani da sashe na 5(b) na dokar da ta kafa NEDC a 2017 a wajen tabbatar da nadin.

Shugaban kasar ya sake bada sunan Janar Paul Tarfa (rtd) ya zarce a majalisar NEDC. Tsohon sojan ya yi karatu da Buhari, ya yi ritaya ne a shekarar 1988.

Kara karanta wannan

Yarbawa Sun Fara Kuka da Tinubu Kan Yawan Fifita Legas Wajen Nada Mukamai

Yayin da Janar Tarfa mai ritaya zai jagoranci majalisar da ke sa ido, an nemi majalisa ta sake tabbatar da Mohammed Alkali a matsayin shugaban NEDC.

Sauran wadanda ake so su koma mukamansu sun hada da Gambo Maikomo, Abdullahi Abbas, Tsav Aondoana, Mutiu Lawal- Areh da Samuel Onuigbo.

Ahmed Yahaya ne zai wakilci Gombe a matsayin Darektan gudanar da ayyuka. Sai dai mutanen jihar da-dama sun ci burin samun shugabancin hukumar.

Wasa ya rikide a APC

Da alama an fasa ba tsohon Gwamnan Kano kujerar Minista, rahoto ya zo cewa Abdullahi Umar Ganduje zai rike jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Hankalin Bola Tinubu da manyan Jam’iyya ya natsu kan Ganduje. Tsohon Gwamnan da da wasu fitattun ‘yan siyasan Osun za shiga cikin majalisar NWC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel