Mutanen Kano Sun Shirya Addu'ar Tunawa da Marigayi Dan Masanin Kano
- Kanawa sun gudanar da taron addu’o’I da tunawa da marigayi Dan Masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule
- A ranar Litinin, 3 ga watan Yuli ne Marigayi Dan Masanin Kano ya cika shekaru 6 da rasuwa
- Malaharta taron sun bayyana Maitama Sule a matsayin abun alfahari arewa wanda ya cancanci ayi koyi da shi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Mazauna jihar Kano da sauran yankunan arewa sun shirya taron addu'a don tunawa da marigayi Dan Masanin Kano, Alhaji Dr. Yusuf Maitama Sule wanda ya rasu shekaru shida da suka gabata.
Idan za ku tuna, Marigayi Dan Masani ya rasu a ranar 3 ga watan Yulin 2017 yana da shekaru 88 a duniya.

Source: UGC
Maitama Sule abun alfaharin arewacin Najeriya
Taron addu'o'in wanda ya gudana a gidan marigayin da ke Kano a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli, ya tuna da rayuwar dan mazan jiyan da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Arewa da ma kasar baki daya, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan
Magana Ta Ƙare: Shugaba Tinubu Ya Ɗora Nauyin Dawo da Zaman Lafiya A Zamfara Kan Mutum 1
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake magana a yayin taron, wani lakcara kuma masanin tarihi, Dr. Aliyu Muri ya bayyana Maitama Sule a matsayin abun alfaharin arewa wanda ya kamata shugabannin yanzu su yi koyi da shi domin ci gaban kasar.
Ya ce yan arewa baki daya za su ci gaba da tunawa da shi domin ya yi wa kasar hidima cike da jajircewa da amana, yana mai bayyana shi a matsayin mai kishin kasa da ya cancanci a tuna da shi a kullun.
Dr Muri ya ce:
"Ko shakka babu Marigayi Dan Masanin Kano alama ne da ke nuni ga rikon amana wanda ya bayar da gagarumin gudunmawa wajen ci gaban Najeriya. Har yanzu ya kasance abun alfahari ga Najeriya. Wannan ne dalilin da yasa ya cancanci a dunga tunawa da shi a kullun kwanan duniya domin shugabanninmu na yanzu su yi koyi da shi."
Da yake jawabi, Rabe Isa Kambarawa daga jihar Katsina, wanda ya rubuta litattafai biyu kan rayuwar marigayi Dan Masani ya ce akwai abubuwa da matasa za su yi a rayuwarsu domin kaiwa matsayin Dan Masani.
Kmbarawa ya kuma ce wannan ne dalin da ya sa ya rubuta takardunsa domin su zama tsani ga matasa da shugabanni.
Da yake jawabi a madadin iyalin marigayin, Dan Masanin Kano mai ci, Abdullahi Yusuf Maitama Sule ya yi godiya ga wadanda suka hallara kan wannan karamci da suka yi masa, yana mai cewa mahaifinsu yana daukar kowa a matsayin nasa.
Shugaban kasa Tinubu bai fadi a wajen taro ba, binciken gaskiya
A wani labari na daban, wani bincike da aka gudanar kan labarin da ke yawo cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya fadi wajen duba sabon ofishin mai ba kasa shawara kan tsaro ya nuna ba gaskiya bane.
Wani bidiyo dai ya bayyana a Facebook inda aka yi ikirarin cewa shugaban kasar ya yi tuntube sannan ya fadi yayin da ya fita rangadi da masu tsaronsa.
Asali: Legit.ng
