Maganin Ganganci: Wata Uwa Ta Gaji da Halin Danta Na Jefar da Jakar Makaranta, Ta Ba Shi Buhun Siminiti

Maganin Ganganci: Wata Uwa Ta Gaji da Halin Danta Na Jefar da Jakar Makaranta, Ta Ba Shi Buhun Siminiti

  • Wata uwa 'yar Najeriya ta jawo cece-kuce a shafin sada zumunta bayan ta ba danta buhun siminti ya yi amfani da shi a matsayin jakar makaranta
  • Da alama dai yaron ba shi da wata jaka, ko kuma tsohuwar ta lalace saboda rashin kulawa da wasa irin na yawa
  • Sai dai yaron bai ji dadi ba bayan da aka mika masa buhun siminti na Dangote a lokacin da ‘yan uwansa mata ke dauke da jakunkuna masu kyau

Wata uwa da ta gaji da siya wa danta jakar zuwa makaranta ta ba shi buhun simintin Dangote ya yi amfani da shi.

An gano mahaifiyar ‘yar Najeriya a cikin wani faifan bidiyon TikTok tana koka cewa tana siyan jaka biyu ga dan nata kowane zangon karatu.

Bayan ta gaji da jigilar saya wa yaron jakar makaranta, sai kawai ta yanke shawarar ba shi buhu ya sanya takardunsa.

Kara karanta wannan

“Neman Halal”: Matashiya Mai Ji Da Tsantsar Kyau Ta Kama Sana’r Tuwo, Bidiyonta Ya Yadu

Yadda aka ba yaro buhu ya tafi dashi makaranta
Lokacin da yaron ke jimamin ba shi buhu | Hoto: @bella_twinnies.
Asali: TikTok

A cikin faifan bidiyon, wanda ya bazu ya kuma haifar da raha, cece-kuce da martanin jama’a, an ga sauran yaran matar duk suna dauke da jakunkuna masu kyau yayin da shi kuwa ta mika masa buhun siminiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya nuna yadda yaron ya yi turjiya bayan ba shi buhun siminiti

Yaron ya ki taba jakar da farko sai ya yanke shawarin zama a gida, ya ki fitowa ya tafi makaranta kamar sauran ‘yan uwansa.

’Yan uwansa mata wadanda su ma suke sanye da kayan makarantarsu, sun roki mahaifiyarsu da ta sake tunani ta ba yaron sabuwar jakar da ta siya, amma ta ki.

Yaron ya fito daga baya ya dauki buhun amma ya ji ba dadi sosai game lamarin. @bella_twinnies ce ta wallafa bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta ta TikTok

Kara karanta wannan

Likita Ya Faɗa Wa Wani Mutumi Kar Ya Kusanci Matarsa Saboda Abu 1, Da Suka Koma Gida Ya Ba Da Mamaki a Bidiyo

@Jennifer ya ce:

"Na tuna lokacin da na batar da jakar makarantata a nursery aji 3 har sau 2 kafin karshen zango, mahaifiyata ta ba ni jakarta a matsayin sabuwar jakar makarantata na yi kuka har na gaji."

@monicanewinsky yayi sharhi:

"Sadda na lura da "jakar makarantar" sai da na kusa suma! Mama me haka?"

@ mai amfani8226502630768 ya ce:

"Haka na yi ta fasa kwanon abinci na har sai da mahaifiyata ta zuba min shinkafa da miya a cikin farar leda. Babu wanda ya sake min fada."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.