DSS ta Raba Emefiele da Fasfon Fita Kasar Waje, Za a Binciki Ofishi da Gidajensa

DSS ta Raba Emefiele da Fasfon Fita Kasar Waje, Za a Binciki Ofishi da Gidajensa

  • Har yanzu Gwamnan babban bankin CBN da aka dakatar ya na hannun jami’an tsaro masu fararen kaya
  • Ana zargin Jami’an DSS sun raba Godwin Emefiele da duk wasu takardunsa na fita kasashen ketare
  • Hakan zai bada dama a binciki Gwamnan na CBN da kyau, kuma jami’ai za su shiga gida da ofishinsa

Abuja - Jami’an hukumar DSS sun karbe takardar fasfon Godwin Emefiele wanda aka dakatar daga kujerar Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN.

A wani rahoto da aka samu daga Punch, an fahimci fasfon Godwin Emefiele bai hannunsa, hakan zai hana shi damar tserewa ne daga kasar nan.

Baya ga haka, an samu labari jami’an tsaron masu fararen kaya za su iya shiga gidaje da ofishin tsohon gwamnan bankin na CBN domin su yi bincike.

Kara karanta wannan

Wasa farin girki: Yadda tun farko Tinubu ya hango Emefiele na masa tuggu a zaben 2023

Godwin Emefiele
Gwamnan CBN da aka dakatar, Godwin Emefiele Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A makon nan ake tunanin DSS za ta shiga laluben wurin aiki da gidan Emefiele da nufin samun hujjoji a binciken jerin zargin da hukuma ke yi masa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Al'adar binciken DSS

Wata majiya da ke DSS ta shaida cewa a al’ada idan aka cafke mutum domin ayi bincike, za a karbe duk takardunsa saboda a hana sa fita Najeriya.

Majiyar ta fadawa jaridar za ayi bincike a ofishin na Emefiele da kuma inda yake zama.

Za a kira Darektocin CBN

Ana haka ne kuma The Cable ta ce labari ya zo cewa za a iya gayyatar manyan Darektocin CBN domin yi masu tambayoyi kan binciken da ake yi.

Wasu Darektocin babban bankin kasar sun taka rawar gani wajen aikata laifuffukan da ake jifan Gwamnan da aka dakatar da aikatawa yayin da yake ofis.

Kara karanta wannan

DSS Ta Jero 'Laifuffukan' Emefiele, Za Ta Bukaci Karin Lokacin Cigaba da Tsare Shi

Daga cikin zargin da ake tunani DSS ta na yi wa gwamnan CBN har da sa hannunsa wajen facaka da dukiya a karkashin tsare-tsaren noma da aka kawo.

Manema labaran sun nemi jin ta bakin Kakakin DSS na kasa, Peter Afunanya, amma ba a iya samunsa ta wayar salula a lokacin da ake hada rahoton ba.

Shugaban Najeriya ya yi jawabi

A jawabin, Mai girma shugaban kasa na tunawa da ranar damukaradiyya, an ji labari ya aika sako da ake tunanin ya shafi Atiku Abubakar da kuma Peter Obi.

Bola Tinubu ya tuna da MKO Abiola da mai dakinsa Kudirat da irinsu Pa Alfred Rewane da Shehu Yar’Adua da suka mutu kan gwagwarmayar zaben 93.

Asali: Legit.ng

Online view pixel