“Na Kashe Shi”: Dan Najeriya Ya Mutu Bayan Dansa Ya Yi Watsi Da Gargadinsa Sannan Ya Kashe Kaguwa

“Na Kashe Shi”: Dan Najeriya Ya Mutu Bayan Dansa Ya Yi Watsi Da Gargadinsa Sannan Ya Kashe Kaguwa

  • Wani dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya tuna yadda mahaifinsa ya mutu
  • Kafin wannan rana da ba zai taba mantawa ba, mahaifinsa yana yawan gargadinsa da kada ya kashe duk wani abu mai rai da zai gani a doron kasa
  • Sai dai kuma, matashin ya gano wata kaguwa a harabar gidansu sannan ya gasa mantawa da abun da ya faru bayan ya kashe ta

Wani dan Najeriya ya bayyana yadda mahaifinsa ya mutu yan awanni bayan ya kashe wata kaguwa da ya gano a harabar gidansu.

A cewar mutumin mai suna @tinny_vanilla a twitter, da misalin karfe 11"00 na dare, ya gano wata kaguwa a harabar gidan sannan bai duba umurnin da mahaifinsa ya yi masa ba.

Hoton mutane dauke da akwatin gawa, kaguwa da wani dattijo
“Na Kashe Shi”: Dan Najeriya Ya Mutu Bayan Dansa Ya Yi Watsi Da Gargadinsa Sannan Ya Kashe Kaguwa Hoto: Junce, MoMo Productions, Zikoko
Asali: Getty Images

Mahaifin nasa na yawan shawartansa da kada ya kuskura ya kashe kowani abu mai rai da zai gani. Sai dai kuma a wannan rana, 8 ga watan Afrilun 2010, ya kashe wata kaguwa sannan ya rasa mahaifinsa washegarin ranar.

Kara karanta wannan

Shin Sabon Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, Ya Ayyana Triliyan N9 a Kadarorinsa? Gaskiya Ta Bayyana

"Mahaifina na yawan umurtana da kada na kashe duk wani abu mai rai da zan gani, karfe 11:00 na 8 ga watan Afrilun 2010 na ga wata kaguwa na tafiya a cikin harabar gidan don haka sai na kashe ta. Washegari da safe mahaifina ya rigada ya mutu..." ya rubuta a twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce yana tuna abun duk lokacin da yake bakin ciki.

"A duk lokacin da nake bakin ciki sai na fara tuna lamarin yadda na dauki ransa."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Kvnq_Jamal ya ce:

"Na taba jin irin wannan labarin lokacin da na ziyarci mahaifina a sansanin sojin ruwa da ke portharcourt. Na zata karya mutumin yake yi shima."

@UncleMohamz ya ce:

"Ina mai baka hakuri za ka ci gaba da zama da wannan tunanin har abada. Da ganin wannan damuwa ce mai nauyi."

Kara karanta wannan

Babban Abokin Faɗan Tinubu Ya Ajiye Kayan Yaƙi, Ya Shirya Zai Karɓi Tayin Kujera

@ewai_bekee ya ce:

"Wannan lamari na kaguwa da mutanen port harcourt 5/6 ne abun dariya ne yadda yake zama gaskiya. Amma me yasa kuke yawan zabar kaguwa? Me yasa ba kare ba akalla zai iya guduwa don tsira da rayuwarsa."

Budurwa da ta hau jirgin sama daga Lagas zuwa Casablanca ta gfadi halin da ta shiga

A wani labari na daban, wata budurwa wacce ta shiga jirgin sama daga Lagas zuwa Casablanca ta ce akwai wani mutum da ke gurbata iskar da suke shaka.

Matashiyar mai suna @iamrenike a Twitter ta koka cewa fasinjan da take magana a kai yana ta tusa akai-akai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel