'Yan Bindiga Sun Sace Wani Babban Faston Katolika a Jihar Imo

'Yan Bindiga Sun Sace Wani Babban Faston Katolika a Jihar Imo

  • Wani faston ɗariƙar Katolika ya haɗu da sharrin miyagun ƴan bindiga a jihar Imo lokacin da suka yi awon gaba da shi
  • Ƴan bindigan sun sace Rev Fr Mathias Opara lokacin da ya ke dawowa daga binne gawar mahaifin wani fasto abokin aikinsa
  • Ƴan bindigan sun kuma tasa ƙeyar sauran mutanen da ke tare da babban faston a cikin motar zuwa cikin daji

Jihar Imo - Ƴan bindiga da yammacin ranar Juma'a sun sace Rev Fr Mathias Opara, wani fasto na ɗariƙar Katolika wanda ya ke a cocin Owerri Catholic Archdiocese.

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa an sace faston ne akan titin hanyar Ejemekwuru- Ogbaku, cikin ƙananan hukumomin Oguta da Mbaitoli a jihar Imo.

Yan bindiga sun sace babban fasto a jihar Imo
'Yan bindigan sun kwamushe faston ne yana kan hanyar dawowa gida Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Faston wanda aka fi sani da Owu Ujo, an ritsa shine lokacin da ya ke dawowa zuwa birnin Owerri, babban birnin jihar a cikin motarsa, bayan ya halarci binne mahaifin wani fasto abokin aikinsa, wanda aka gudanar a Izombe cikin ƙaramar hukumar Oguta ta jihar Imo.

Kara karanta wannan

Rabona Da Bikin Ranar Haihuwa Tun Dauke 'Yan Matan Chibok, Cewar Tsohon Minista

An sace faston yana kan hanyar dawowa gida

Wani majiya ya tabbatar da cewa, lamarin ya auku ne a gabansu lokacin da su ke kan hanyar dawowa daga binne gawar mahaifin wani fasto a Izombe, cikin ƙaramar hukumar Oguta ta jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"An sace Rev. Fr. Mathias Opara wanda aka fi sani da Owu Ujo akan titin hanyar Ejemekwuru/Ogbaku. An yi awon gaba da shine tare da sauran waɗanda su ke a cikin mota ɗaya."
"Lamarin ya auku ne akan idanunmu. Mu ma muna dawowa ne zuwa Owerri daga binne gawar mahaifin wani faston ɗariƙar Katolika a Izombe, cikin ƙaramar hukumar Oguta."

Darektan watsa labarai na Owerri Catholic Archdiocese, Rev Fr Raymond Ogu, ya tabbatar da sace faston, cewar rahoton The Punch.

Yan Bindiga Sun Sace Shahararren Malamin Addini a Adamawa

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Ɗalibin Jami'a a Najeriya Ya Faɗi Ya Mutu Ana Tsaka da Wasan Kwallo

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani shahararren fasto mai gudanar da wa'azi a gidan talbijin a jihar Adamawa.

Ƴan bindigan sun bi Rabaran Mike Achigbo, wanda shine shugaban cocin Freedom Power Chapel, har gidansa da ke a yankin Nyibango sannan suka tasa ƙeyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel