Rabona Da Bikin Ranar Haihuwa Tun Dauke 'Yan Matan Chibok, Cewar Tsohon Minista

Rabona Da Bikin Ranar Haihuwa Tun Dauke 'Yan Matan Chibok, Cewar Tsohon Minista

  • Tsohon ministan yaɗa labarai a lokacin Jonathan, Edwin Clark, ya ce tun lokacin da aka sace 'yan matan Chibok ya daina bikin zagayowar ranar haihuwarsa
  • Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a gidansa da ke Abuja a lokacin da yake bikin cikarsa shekaru 96 da haihuwa a duniya
  • Ya kuma ce akwai buƙatar samun haɗin kai a Najeriya, domin idan babu haɗin kai ba za a samu ci-gaban da ake buƙata a ƙasa ba

Abuja - Tsohon ministan yaɗa labarai, Cif Edwin Clark ya ce ya daina bikin zagayowar ranar haihuwarsa tun lokacin da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok da ke jihar Borno.

Idan za ku iya tunawa sama da ɗalibai 200 na sakandiren ’yan mata da ke garin Chibok, ‘yan bindiga suka sace daga ɗakin kwanan ɗalibai a ranar 14 ga watan Afrilun 2014.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce a cikin gida da ma wajen ƙasa inda, shugabanni da masu fafutuka suka matsawa gwamnatin Najeriya lamba kan ta ceto 'yan matan.

Edwin Clark ya ce rabonsa da murnar zagayowar ranar haihuwa tun da aka sace yan matan Chibok
Edwin Clark ya ce rabonsa da murnar zagayowar ranar haihuwa tun da aka sace yan matan Chibok. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sace 'yan matan Chibok abu ne mara daɗi

Daily Trust ta ruwaito cewa Edwin Clark ya yi jawabin ne da ma wasu jawabai ranar Alhamis a gidansa da ke Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi a wajen bikin cikarsa shekaru 96 a ranar Alhamis, gaban manyan 'yan siyasa da suka halarci bikin, Clark ya ce tun faruwar lamarin bai ƙara yin bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba, domin abu ne mai matuƙar muni, mara daɗi da ya faru da ƙasar.

Clark, wanda shine shugaban ƙungiyar zauren 'yan Neja-Delta (PANDEF), ya ce:

“Na daina bikin zagayowar ranar haihuwata tun lokacin da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok da ke jihar Borno. Abin da matuƙar ciwo.”

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

Yau ma ba bikin zagayowar ranar haihuwar na yi ba

Ya kuma ce ko a wannan karon ma ba wai ya yi bikin zagayowar ranar haihuwa tasa ba ne, ya dai yi taron ne domin godewa Ubangiji.

A kalamansa:

“Yau ba biki nake yi ba, ina godewa Ubangiji ne. Ba na yin bikin ne saboda na rasa ƙanne na guda biyu a baya.”

Da yake ci-gaba da jawabi, Edwin Clark ya bayyana cewa yanzu babu haɗin kai a tsakanin 'yan Najeriya, wanda kuma ya samo asali ne daga rashin amana da yarda da juna.

Ya kuma bayyana cewa ba za a samu zaman lafiya ba idan babu haɗin kai a tsakanin 'yan ƙasa.

Sai da haɗin kai Najeriya za ta ci-gaba

Ya ƙara da cewa Najeriya ba za ta taɓa ci-gaba ba idan ba a samu haɗin kan 'yan ƙasar ba. Clark ya kuma ce ba za su yi shiru suna ganin 'yan ƙasa na shan wahala ba, dole ne su yi magana.

Kara karanta wannan

Farfesa Isa Pantami Ya Fara Shirye-Shiryen Sauka Daga Kujerar Ministan Sadarwa, Bayanai Sun Fito

A rahoton jaridar Leadership, Clark ya ce Arewa suna bukatar yankin Kudu, haka nan ma 'yan Kudu suna da bukatar 'yan Arewa.

Da yake jawabi a lokacin bikin, gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya nuna farin cikinsa cewa Clark har yanzu da yake da shekaru 96 yana kira a kan haɗin kai.

Haka nan ya yi farin ciki cewa har yanzu yana iya tunawa da tarihin abubuwan da suka faru a Najeriya tare da lokutan da suka faru.

An samu ƙarin 'yan matan da suka gudo daga hannun 'yan ta'adda

A wani labarin da muka wallafa a kwanakin baya, an samu ƙarin 'yan mata biyu da suka kuɓuto daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram.

'Yan matan dai sun kasance cikin 'yan mata sama da 200 da 'yan ta'addan suka sace a 2014, daga ɗakin kwanansu da ke makarantar sakandiren 'yan mata da ke Chibok jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel