Dalibin Jami'a A Najeriya Ya Mutu a Filin Kwallo, Dalibai Sun Ta Da Hargitsi

Dalibin Jami'a A Najeriya Ya Mutu a Filin Kwallo, Dalibai Sun Ta Da Hargitsi

  • Ɗaliban jami'ar Benson Idahosa da ke Benin, babban birnin jihar Edo, sun ɓarke da zanga-zanga ranar Talata
  • Rahoto ya nuna cewa ɗaliban sun yi ɓarna yayin nuna fushinsu bisa mutuwar abokin karatunsu wanda ya yanke jiki a filin ƙwallo
  • Hukumar makaranta ta bayyana cewa nan gaba kaɗan zata fitar da cikakken jawabi kan lamarin a hukumance

Edo State - Ɗaliban jami'ar Benson Idahosa, Benin, babban birnin jihar Edo, sun fantsama cikin harabar makaranta suna zanga-zangar nuna fushi ranar Talata.

Daily Trust ta rahoto cewa ɗaliban sun ɓarke da zanga-zanga ne sakamakon mutuwar abokin karatunsu a jami'ar mai suna, Bruno Chigozie Ezeonye.

Jami'ar Benson Idahosa.
Dalibin Jami'a A Najeriya Ya Mutu a Filin Kwallo, Dalibai Sun Ta Da Hargitsi Hoto: dailytrust

Marigayi dalibin, wanda ke shekarar ƙarshe a Kwas ɗin 'Computer Science' ya yanke jiki ya faɗi yana tsaka da buga wasan kwallo a filin wasanni, daga bisani rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Gwamnatinsa Ta Gina Jami'ar Sufuri a Mahaifarsa Daura

Wata majiya daga cikin ɗaliban ta ɗora laifi kan Likitocin jami'ar sakamakon rashin duba shi cikin hanzari yayin da aka gaggauta garzayawa da shi Asibiti don ceton rayuwarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ta ce:

"Lokacin da suka zo kansa suka buƙaci a gaggauta kai shi Asibitin Faith Mediplex da ke kan Titin zuwa filin jirgi, mai alaƙa da jami'ar, sai Direban motar Ujila ya ce babu mai a motar."

Meyasa ɗaliban suka yi zanga-zanga?

Sakamakon mutuwar ɗalibin ne, abokan karatunsa na jami'ar suka ɓarke da zanga-zanga, suka lalata muhimman wurare domin nuna fushinsu da halayyar jami'an lafiya.

Yayin haka ne ɗaliban suka lalata ɗan karamin Asibitin cikin makaranta da kuma ofishin jami'an tsaron jami'ar daga bisani shugaban jami'ar, Bishop FEB Idahosa, ya samu nasarar kwantar masu da hankali.

Wane mataki hukumar makarantar ta ɗauka?

Yayin da aka tuntuɓe shi, shugaban sashin sadarwa da dabaru na jami'ar, Temi Esonamunjor, ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bola Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Firaministan Burtaniya, Bayanai Sun Fito

"Hukumar makaranta zata fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba."

"Ba Mu Bane" EFCC Ta Ankarar da 'Yan Najeriya Kan Sabon Salon Damfara da Ya Bullo

A wani rahoton na daban kuma EFCC ta ankarar da 'yan Najeriya kan wata sabuwar hanyar damfara da aka bullo da ita da sunan EFCC.

A wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar, ya buƙaci yan Najeriya sun guji saƙon da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da sunan, 'EFCC Helf Desk.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel