Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

  • Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC ta gurfanar da wani dattijo kan laifin ɓata kuɗin ƙasa
  • Jami'an hukumar NDLEA ne suka fara kama mutumin wanda a yayin gudanar da bincike ne suka gano tsabar kuɗaɗe a tattare da shi
  • Mutumin ya bayyana cewa sama da shekaru 25 kenan da yake wannan sana'a ta sarrafa tsabar kuɗaɗe zuwa kayan ado

Jihar Kano - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon kasa (EFCC) reshen jihar Kaduna, ta gurfanar da wani dattijo a gaban kotu.

EFCC ta dai gudanar da mutumin mai suna Ibrahim Musa Dabai a gaban mai shari’a M.N Yunusa na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano.

Kotu ta tura wani dattijo gidan yari saboda laifin tozarta kudi
Kotu Ta Tura Wani Dattijo Zuwa Gidan Yari Saboda Laifin Ɓata Kuɗin Najeriya. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Ana tuhumarsa da tozarta kuɗin Najeriya

EFCC ta tuhumi mutumin ne da laifin tozartar da kuɗaɗen Najeriya, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Mutane Hudu Sun Faɗa Komar ‘Yan Sanda a Ogun Bisa Laifin Halaka Makiyayi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) suka fara kama Mista Ibrahim a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A yayin gudanar da bincike ne suka same shi tare da tsabar kuɗi da ya yi ikirarin cewa yana amfani da su ne wajen yin kayan ado domin siyarwa.

Bayan hakan ne, hukumar ta NDLEA suka miƙa shi zuwa hannun hukumar EFCC domin ci-gaba da bincike.

Shekaru 25 ya yi yana sana'ar sarrafa tsabar kuɗi

A yayin gudanar da bincike, mutumin da aka yankewa hukuncin ya bayyana cewa ya shafe shekaru 25 yana sana’ar canza tsabar kudi zuwa kayan ado da suka haɗa da zobe, ‘yan kunne, mundaye da sauransu.

Laifin ya ƙara da cewa,

“Kai Ibrahim Musa Dabai wani lokaci a cikin watan Maris, 2023 a Kano, a ƙarƙashin ikon babbar kotun tarayya, bisa rajin kanka, ka yi ta’ammali da kuɗin Najeriya : tsabar kuɗi da babban bankin Najeriya (CBN) ya samar, a lokacin da ka yi amfani da su domin ƙera kayan ado domin yin kasuwanci, don haka ka aikata laifi da ya sabawa sashe na 21 (1) na dokar babban bankin Najeriya ta 2007”.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: EFCC Ta Ja Hankalin Yan Najeriya Kan Wata Sabuwar Barazana da Ta Ɓullo

Ibrahim ya kuma amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Lauyan masu shigar da kara, N. Salele ya buƙaci kotun da ta hukunta wanda ake tuhuma bisa laifin da ya aikata.

Mai shari’a Yunusa, ya yankewa mai laifin hukuncin ɗaurin watanni 3 a gidan yari ko kuma tarar Naira 30,000.

Bugu da ƙari, za a mayar da kuɗaɗen da ya riga ya sarrafa zuwa ga babban bankin Najeriya (CBN), domin a lalata su kamar yadda dokar CBN ta 2007 ta tanada.

Gwamnan APC ya nemi EFCC ta binciki muƙarraban Buhari

A wani labarin mu na baya, gwamnan jihar Zamfara ya buƙaci EFCC ta binciki duka muƙarraban gwamnatin shugaba Buhari mai barin gado.

Gwamnan na jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi wannan kira ne bayan wani saƙo da hukumar ta EFCC ta aika masa kan cewa za ta binciki gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel