Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Zababben Gwamna da Wasu Yan Takara a Kano da Abia

Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Zababben Gwamna da Wasu Yan Takara a Kano da Abia

  • Babbar Kotun tarayya ta rushe tikitin takarar gwamnan Abiya mai jiran gado, Alex Otti, da sauran yan takarar LP a jihar da kuma Kano
  • Mai shari'a Yunusa ya bayyana cewa baki ɗaya kuri'un da 'yan takarar suka samu a zaben 2023 ba su da amfani
  • Wannan hukunci na zuwa ne kwana 10 kacal gabanin rantsar da waɗanda suka samu nasara a babban zaben da aka kammala

Kano - Babbar Kotun tarayya mai zama a birnin Kano ta rushe tikitin takarar zababben gwamnan jihar Abiya, Dakta Alex Otti, na jam'iyyar Labour Party (LP).

Haka zalika Kotun ta kuma rushe takarar baki ɗaya 'yan takarar da jam'iyyar LP ta tsayar a jihohin Kano da ke Arewa Maso Yamma da Abiya, Kudu maso Gabas.

Alex Otti.
Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Zababben Gwamna da Wasu Yan Takara a Kano da Abia Hoto: channelstv
Asali: UGC

Mai shari'a Mohammed Yunusa na babbar Kotun tarayya ne ya sanar da haka yayin yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar gabansa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Muhimman Abu 2 da Suka Jawo Allah Ya Hana Atiku da Peter Obi Mulkin Najeriya a 2023

A cewar Alkalin babbar Kotun, ayyana su a matsayin 'yan takara karkashin inuwar LP ya saɓa wa tanadin kundin dokokin zaɓe 2022.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne a ƙara mai lamba FHC/KN/CS/107/2023, wacce Ibrahim Haruna ya shigar yana tuhumar LP da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC).

"Ba zai yuwu jam'iyyar siyasan da ta karya tanadin kundin dokokin zaɓe kuma ace tana da ɗan takara a wani zabe ba balle har a ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara."

"Bisa la'akari da haka, baki ɗaya kuri'un da aka kaɗa wa wanda ake tuhuma na farko sun zama mara amfani," inji mai shari'a Yunusa, kamar yadda Punch ta rahoto.

Alkalin ya kara da cewa Kotu ta soke tikitin baki ɗaya 'yan takarar LP a Kano da Abiya ne saboda gazawar jam'iyyar wajen miƙa sunayen mambobinta masu rijista ga INEC kwana 30 gabanin zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Gwamnonin Arewa Na APC Sun Bayyana Matsaya Kan Shugabancin Majalisa Ta 10

Ku Jira Hukuncin Kotu Kafin Halatta Nasarar Bola Tinuhu, Obi Ga Amurka

A wani rahoton kun ji cewa Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP ya maida martani ga ƙasar Amurka kan kiran Tinubu ta wayar tarho.

A cewar Peter Obi, bai kamata Amurka ta aminta da halascin nasarar Tinubu ba har sai lokacin da Kotun zaɓe a Najeriya ta yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262