Aisha Buhari: Bai Kamata Shugaban Kasa Ya Sake Fita Kasashen Waje Don Neman Magani Ba

Aisha Buhari: Bai Kamata Shugaban Kasa Ya Sake Fita Kasashen Waje Don Neman Magani Ba

  • Aisha Buhari, uwar gidan shugaban kasa ta ce yanzu babu wani shugaba da zai sake fita waje neman magani
  • Aisha ta bayyana haka ne a yayin kaddamar da asibitin gidan gwamnati da aka gudanar a ranar Juma’a a Abuja
  • Ta ce asibitin zai kula da akalla mutane 35,000 inda ta ce asibitin zai rage yawan fitar da shugabanni ke yi neman lafiya

FCT, Abuja - Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bayyana cewa asibitin da mai gidanta Buhari ya kaddamar a gidan gwamnati zai taimaka wurin hana zuwa kasashen waje da shugabannin kasa ke yi neman magani.

Shugaba Buhari ya kaddamar da asibitin ne na N21bn a ranar Juma’a 19 ga watan Mayu a birnin tarayya Abuja.

Aisha Buhari da Shugaba Buhari wurin kaddamar da asibiti
Aisha Buhari ta ce shugabanin kasa nan gaba ba sai sun tafi kasashen waje duba lafiyarsu ba. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Cikas 1 da Ya Hana Ni Maganin Barayin Gwamnati a Mulkina

Aisha Buhari ta yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da asibitin inda ta ce samun wannan asibiti zai rage yawon shugabannin kasa da iyalansu zuwa kasashen waje neman lafiya, jaridar Tribune ta tattaro.

Ta ce ta kawo shawarar samar da asibitin ne shekaru shida da suka gabata ganin yadda mijinta ya dade a kasashen ketare don neman lafiya, ta kara da cewa yanzu abun da ya rage akwai shine su kawo kwararrun likitoci da za su taimaka a harkar lafiyar kasar.

A rahoton Channels, da take amsa tambaya akan asibitin, Aisha Buhari ta ce:

“Ina cikin murna, na cika buri na, duk da muna shirin barin gwamnati amma ina murna mun kaddamar da shi.
“Ni na ba da shawarar hakan shekaru shida da suka gabata, lokacin da mijina ya shafe watanni uku a kasar waje, kuma bai kamata ba, muna da kwararru a kasar, kawai yanayi mai kyau muke bukata.”

Kara karanta wannan

Bai Kamata Ku Tsaya Binciken Gwamnatocin Baya Ba, Shawarin Umar-Radda Ga Zababbun Gwamnoni

Aisha Buhari ta fadi yawan mutanen da asibitin zai kula da su

A cewarta:

“Asibitin zai kula da iyalan shugaban kasa ne amma akalla mutane 35,000 za su amfana da shi. Shiyasa na dage don ganin an samar da bangaren manyan mutane kusa da gidan gwamnatin.”

Ta kara da cewa:

“Asibitin zai taimaka wurin hana shugaban kasa da iyalansa fita waje don neman lafiya, abin da ake bukata kawai shine kawo kwararru da za su taimaka wa mutanen mu.
“Bai kamata wani shugaba ya sake shafe watanni a kasar waje ba don neman magani.”

Aisha Buhari Na Daga Cikin Masu Hana Ruwa Gudu a Gwamnatin nan - Inji Naja’atu Mohammed

A wani labarin, tsohuwar daraktan gangamin yakin neman zaben APC, Naja'atu Mohammad ta ce Aisha Buhari na daga cikin masu hana ruwa gudu a kasar.

Naja'atu ta ce tun bayan hawan gwamnatin, matar ke kitse-kitsen ta don cimma burinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel