Mahaukaci Ya Sha da Kyar Bayan Dan Sanda Ya Biyo Wani Direban Mota a Jihar Niger

Mahaukaci Ya Sha da Kyar Bayan Dan Sanda Ya Biyo Wani Direban Mota a Jihar Niger

  • Mahaukaci ya sha da kyar bayan wani direban babban mota ya nufo shi a kokarin kaucewa kamun dan sanda
  • Jami’in dan sandan ya biyo direban ne tun daga kauyen Paiko dake kan hanyar Minna zuwa Abuja
  • Yaron motar ya ce ‘yan sandan sun ki karbar N1000 na kudin goro wanda hakan ne ya jawo suka gudu

Jihar Niger - Wani mahaukaci ya tsallake rijiya da baya a shataletalen Kpakungu a Minna babban birnin jihar Niger a ranar Laraba 17 ga watan Mayu.

Mahaukacin wanda ke kwance a bakin hanya ya sha da kyar ne bayan wani direban babbar mota kirar Mitsubishi dauke da kayan gwari ya nufo kansa a kokarin kaucewa kamun jami’in dan sanda.

Mahaukaci/Jihar Niger
Mahaukaci Ya Sha da Kyar Bayan Wani Direban Mota Ya Kuskure shi a Jihar Niger. Hoto: TheCable
Asali: Facebook

Jami’in dan sandan ya biyo direban ne tun daga kauyen Paiko akan hanyar Minna zuwa Abuja saboda yaki ba da kudin goro da aka tsaida shi.

Kara karanta wannan

Buhari Ba Shi da Asusun Banki Ko Daya Dake Shake da Kudin Haram, in Ji Garba Shehu

An tsare direban motan a ofishin 'yan sanda

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kafin gudun nashi an tsare direban a ofishin ‘yan sanda na shiyyar Kpakungu inda suka bukaci ya ba da kudin goro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaron motar direban mai suna Abubakar Adamu ya bayyana yadda abin ya faru:

“Yan sanda sun bukaci mu basu kudi, sai muka basu N500 amma sai suka ki karba, mu ka kara zuwa N1000 duk da haka suka ki karba.
“Sai muka gudu ‘yan sandan suka biyo mu har cikin Minna, inda muka kusa yin hatsari da kuma kuskuran wani mahaukaci da yake barci a bakin titi.”

Halin 'yan sanda ne karbar kudi, inji yaron mota

Ya kara da cewa:

“Wannan shi ne abin da suke mana kullum, karban kudi babu dalili, mun kai kwana biyu muna kan hanya, mun kashe kudadenmu a gyaran mota kuma tun daga Azare muke zuwa Lagos gashi kayan gwari muka dauko.”

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

Direbobi sun dauki mataki

A dalilin haka, direbobin manyan motoci sun tare hanyar Minna zuwa Bida daga shataletalen da misalin karfe 9 na safe suna neman a saki abokin aikinsu daga komar ‘yan sanda.

Kokarin neman karin bayani daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura saboda wayarsa ba ta shiga ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Yan Ta'adda Sun Yi Awon Gaba da Dagaci da Wasu Mutane 3 a Jihar Niger

A wani labarin, 'yan sanda a jihar Niger sun tabbatar da sace wani digaci a kauyen Dugge da 'yan bindiga suka yi a jihar.

Sanarwar ta ce digacin mai suna Abdullahi B. Zaure an sace shi ne da wasu mutane guda tara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel