Akwai Kudi: Gwamnati Na da Arzikin Karawa Ma’aikata Albashin da Ake Biya Inji Minista

Akwai Kudi: Gwamnati Na da Arzikin Karawa Ma’aikata Albashin da Ake Biya Inji Minista

  • Festus Keyamo, SAN ya ce ba Bola Tinubu za a bari da rikici a sabon karin albashi da aka yi ba
  • Ministan kwadago da samar da ayyukan yin Najeriyan ya ce ma’aikata sun cancanci karin kudi
  • Keyamo ya ce gwamnati mai zuwa ta na da hanyoyin da za ta samu dukiyar aiwatar da kasafin kudi

Abuja- Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo, SAN ya kare gwamnatin tarayya a kan karin albashin da tayi wa wasu.

A karshen makon jiya, Punch ta fitar da rahoto inda aka ji Mista Festus Keyamo yana cewa babu laifi idan gwamnatin Najeriya tayi wa wasu karin albashi.

Gwamnatin tarayya ta karawa ma’aikata 144, 766 karin albashi, wasu su na ganin Muhammadu Buhari ya na neman ya jikawa Bola Tinubu aiki ne.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

Buhari
Shugaban Najeriya Hoto: theyesng.com
Asali: UGC

Festus Keyamo SAN ya sha bam-bam da masu wannan ra’ayi, da jaridar tayi hira da shi a garin Abuja, ya nuna karin ba zai gagari gwamnatin tarayya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan yake cewa ba tarko gwamnatinsu ta shiryawa wanda za su gaje su a mulki ba.

A game da inda za a samo kudin da za a rika biyan ma’aikatan, Lauyan ya ce janye tallafin mai da za a iya zai sa gwamnati ta samu sauki a kasafin kudi.

"Ba za a ce babu dalilin fito da sabon tsarin albashi ba, lura da yanayin da mu ke ciki a Najeriya. Asali ma ma’aikata sun cancanci abin da ya fi haka.
Matsalar ita ce yadda za a tatso kudin. Ina tunani idan gwamnati mai zuwa ta cire tallafi da wasu abubuwa a kasafin kudinmu, gwamnati za ta iya biya.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

- Festus Keyamo SAN

Hakan na zuwa ne bayan ma’aikatan da ke karbar albashi a karkashin tsarin kudi na CONPSS sun samu kari, har da biyansu bashin karin wasu watannin baya.

Rahoton ya ce a baya Chris Ngige wanda shi ne babban Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, ya nuna hikimar da ta sa aka kara albashin ma’aikatan.

'Yan Akpabio/Barau sun kai 69

An rahoto Sanata Godswill Akpabio yana mai cewa a yau adadinsu ya kai kusan 69 kuma kullum magoya bayansa na karuwa, ana sa ran adadinsu ya kai 85.

Akpabio ya zargi wasu abokan takaransa da amfani da kudi, ya ce Majalisar dattawa dauke ta ke da mutane masu daraja, ba za su taba bari a saida Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel