Kotu Ta Tasa Keyar Jami'in Bogi Na EFCC Zuwa Gidan Gyaran Hali

Kotu Ta Tasa Keyar Jami'in Bogi Na EFCC Zuwa Gidan Gyaran Hali

  • Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa tayi nasarar kama wani wanda ake zargin bayyana kansa a matsayin jami`inta
  • Bayan haka, ana zarginsa da damfarar mutane da dama da suka hada da wani dan kasar Belgium fiye da N20m.
  • Tuni kotun ta tusa keyarsa zuwa gidan gyaran hali bayan lissafo laifukansa wadanda suka hada da mallakar dakardun bogi da damfara ta hanyar amfani da yanar gizo.

Jihar Legas - Wata a kotun hukunta laifuka na musamman a jihar Legas ta garkame wani wanda ake zargi da bayyana kanshi a matsayin jami`in hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC.

Wanda ake zargin mai suna Ume Clinton an tura keyarsa zuwa gidan yari na tsawon shekara daya bayan ya damfari wani dan kasar Belgium Yuro 45,000.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Zariya, Sun Kashe Mutum 2 Da Sace Wasu 4

koyun kasa
Alkalin kotu ta yanke wa jami'in EFCC na bogi hukuncin daurin shekara daya a gidan maza. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotu, Mai shari`a Mojisola Dada ce ta yanke wannan hukunci bayan lissafo laifukansa da suka hada da damfara da mallakar takardun bogi wanda hukumar ta kama shi dasu, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Ofishin shiyya na jihar Lagos ce ta tisa keyar Clinton mai shekaru 30, bayan ya damfari dan kasar Belgium Axelle Mahieu makudan kudade.

Me ake zarginsa?

Ana zarginsa da damfara ta hanyar amfani da yanar gizo, wadda yanzu ya zama ruwan dare kuma hanyar da mafi yawan masu laifuka ke amfani dashi don damfarar mutane.

A baya ma an taba gurfanar dashi

An taba gurfanar da wanda ake zargin a gaban Mai shari`a Dada tun a watan Fabrairu na wannan shekara bayan laifukan da ake zarginsa akai suka rinjayi shaidun da aka gabatar wanda hakan yasa aka yi gyara akan laifukan da ake zarginasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Fara Shirye-shiryen Cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa

Clinton ya ce ya arce na tsawon lokaci ana nemasa ba`a same shi ba, amma daga karshe masu binciken sukayi amfani da fasaha suka zakulo shi a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, a Isheri da ke jihar Lagos.

Yan Sanda a Jihar Kogi Sunyi Nasarar Kwamushe Kasurgumin Mai Garkuwa Da Ya Addabi Jama'a

A wani labarin, Rundunar `yan sandan jihar Ekiti ta ce jami`anta sunyi nasarar kama kungurmin mai garkuwa da mutane da ya addabi yankunan jihar.

Kwamishinan yan sanda na jihar, Dare Ogundare ne ya bada wannan sanarwar a ranar Laraba 3 ga watan Mayu lokacin da ya kai ziyara wa kakakin majalisar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel