An Bukaci Tsohon Shugaban Kasa Ya Nemi Afuwar Kabilar Ibo Kan Ta’asar da Ya Aikata, an Fadi Dalili

An Bukaci Tsohon Shugaban Kasa Ya Nemi Afuwar Kabilar Ibo Kan Ta’asar da Ya Aikata, an Fadi Dalili

  • Kabilar Ibo ta bukaci tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya nemi afuwarsu kan rawar da ya taka a yakin Biafra
  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ita ta tura wannan bukata ga tsohon shugaban kasar a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 25 ga watan Faburairu
  • Sakataren kungiyar Mazi Okechukwu Isiguzoro ya ce bayanan da Gowon ya yi ga Tinubu kan yakin Biafra ya dawo musu da sabon ciwo a zuciyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta kabilar Ibo ta bukaci tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ya nemi gafara a gare su.

Kungiyar a bukaci hakan ne daga tsohon shugaban kasar bayan yakin basasa da ya jefa kabilar a gida da waje cikin mummunan yanayi.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa ya ce sun batawa yan Najeriya lokaci, ya fadi tsarin mulkin da ya dace da kasar

Kabilar Ibo ta tura muhimmiyar bukata ga tsohon shugaban kasa
Kabilar Ibo ta bukaci neman afuwa daga Yakubu Gowon. Hoto: Ohanaeze Ndigbo, Yakubu Gowon.
Asali: Facebook

Menene Ndigbo ta ce kan Gowon?

Ohanaeze ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Lahadi 25 ga watan Faburairu, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren kungiyar Mazi Okechukwu Isiguzoro ya ce bayanan da Gowon ya yi ga Tinubu kan yakin Biafra ya dawo musu da sabon ciwo a zuciyarsu.

Isiguzoro ya ce yadda Gowon ya zabi wasu kalmomi a bayanin nasa kan yakin basasar bai kamata ba kuma ya kona wa kabilar rai, cewar Daily Post.

Bukatar da kungiyar ta nema daga Gowon

A cewar sanarwar:

“Dangane da kalamai marasa dadi da tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ya yi kan yakin Biafra, Ibo sun bukaci neman afuwa da sulhu wanda shi zai fara.
“A cikin kalamansa yayin ziyarar da ya kai wa Tinubu ya sake dawo da ciwon da kabilar Ibo suka ji lokacin yakin inda ya furta kalaman da ba su dace ba.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 bayan nasarar Kwankwaso a kotu, uban NNPP ya nemi hadin kai kan abu 1 game da Tinubu

“Kungiyar Ohaneze ta kalubalanci Gowon ta dauki alhakin abin da ya aikata tare da neman afuwar kabilar Ibo da ya tarwatsa.”

Kungiyar har ila yau, ta ce ci gaba da rayuwar Gowon a yanzu da kabilar Ibo fiye da miliyan uku ke kallonsa da rawar da ya taka dama ce da ya kamata ya nemi afuwa.

Gowon ya gana da Tinubu

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya yi ganawa ta musamman da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Wannan ita ce ganawa ta farko da tsohon shugaban ya yi da Tinubu tun bayan hawansa karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel