Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da 4 a Zariya

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da 4 a Zariya

  • Tsagerun yan bindiga sun kai kazamin hari yankin Kofar Kona da ke garin Zariya, jihar Kaduna
  • Maharan sun halaka wasu bayin Allah biyu da ke kan hanyarsu ta wuce sannan suka yi awon gaba da wasu
  • Yan bindigar sun kuma sace mutane masu yawan gaske a kauyen Dorayi amma suka watsar da su bayan an bude masu wuta

Kaduna - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewar an tsinci gawarwakin wasu mutane biyu a daren ranar Litinin lokacin da wasu da ake zaton yan bindiga ne suka farmaki yankin Kofar Kona da ke garin Zariya, jihar Kaduna.

Majiyoyi sun bayyana cewa tsagerun yan bindigar dauke da makami sun isa yankin ne a kafa da misalin karfe 9:40 na dare sannan suka garzaya gidan wani jami'in hukumar kwastam.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cika Hannu Da Yan Sara-Suka 98 a Wata Jihar Arewa

Taswirar jihar Kaduna
Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da 4 a Zariya Hoto: Punch
Asali: UGC

Yadda yan bindiga suka farmaki wasu mazauna Zariya

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yan bindigar wadanda suka zo su da yawa sun farmaki gidan wani jami'in kwastam, Malam Abubakar Modibbo sannan suka yi garkuwa da matarsa Asiya Abubakar da yaranta mata su biyu, Khadijatul Kubra da Hafsat, da kuma wani Falalu Ibrahim.
"Yan bindigar sun kuma harbe wani Zaharaddeen Mohammed na Amaru da Sunusi Sani na Dorayi wadanda suke wucewa.
"Daga bisani an samu labarin mutuwar Sani da safe a asibiti sakamakon raunukan da ya samu daga harbin bindiga."

Wani dan kungiyar yan sa kai ya ce yan bindigar wadanda suka gaggauta garzayawa kauyen Dorayi a wajen garin Zariya sun yi fashin shanu. A cewarsa, sun kuma sace mutane da dama kimanin su 20.

Ya ce yan bindigar sun yi watsi da dukkanin mutanen da suka sace a yankin sannan suka tsere jeji, bayan musayar wuta da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kashe yaran da suka sace a Arewa, sun sako wasu 70

Dan bangar ya bayyana cewa yan bindigar sun kona gidan wani Alhaji Dalha da babura biyu kafin suka tsere saboda zazzafan musayar wuta.

Martanin yan sanda

Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya ci tura don wayoyinsa sun ki shiga.

Jami'an tsaro sun kama bindigogi a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa jami'an rundunar yan sanda a jihar Kano sun kama wasu bindigogin AK-47 guda hudu da aka yi kokarin fasa kaurinsu a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel