Surukar Kirki: Matar Aure Ta Taka Rawa Da Girgijewa Don Murnar Ziyarar Da Uwar Mijinta Ta Kawo Mata

Surukar Kirki: Matar Aure Ta Taka Rawa Da Girgijewa Don Murnar Ziyarar Da Uwar Mijinta Ta Kawo Mata

  • Wani bidiyo da ke nuna shakuwar da ke tsakanin wata uwar miji da surukarta ya yadu a TikTok
  • A cikin bidiyon, an gano matashiyar tana taka rawa jim kadan bayan isowar surukarta wacce ta kawo mata ziyara
  • Su dukka biyun sun rungume junansu wanda hakan ke nuna shakuwar da ke tsakanin uwar mijin da matar dan nata

Wata matar aure da ke matukar kaunar uwar mijinta ta taka rawa jim kadan bayan isowarta gidansu don yin kwana biyu da su.

Matar wacce ta cika da farin ciki ta gaza boye murnarta yayin da ta taka rawa iri-iri, tana girgijewa don nuna yadda ta ji dadin ganinta.

Uwar miji da surukarta
Surukar Kirki: Matar Aure Ta Taka Rawa Da Girgijewa Don Murnar Ziyarar Da Uwar Mijinta Ta Kawo Mata Hoto: @nenyenwa
Asali: TikTok

Uwar mijin wacce itama ta ji dadin hakan ta taya surukar tata takawa cikin murna.

Uwar mijin wacce ta fahimci muhimmancin kyauta ta zo da kayan abinci iri-iri wanda ga dukkan alamu yana daga cikin abubuwan da ya sa matashiyar farin ciki.

Kara karanta wannan

"Almubazaranci": Budurwa Ta Yi Tafiya Ta Kan Kwai, Ta Fasa Wasu, Bidiyon Ya Yadu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewar matar ta yi sa'ar samun suruka da ke sonta.

Bidiyon ya ja hankali sosai a TikTok kuma ya samu dubban mutane da suka danna 'likes'.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Angelabright ta yi martani:

"Wow ina fatan ta kawo utara akpu idan ta kawo wannan nawa ne faaa."

@ChlzorbaUnaeze ta ce:

"Allah ya albarkaci dukkanin iyayen mazajenmu da iyayenmu suma."

@Chommny ta rubuta:

"Dan Allah ki gaishe mana da ita. Iyayen miji nagari suna da wuyan samu. Itama uwarki ce shikenan."

@omoteahon ta yi martani:

"Na so ace uwar mijina ma haka take."

@user1786530283916:

"Iyayen miji na gari babban ni'ima ne."

@Cute363773:

"Ina bin shafinki ne saboda soyayyar da kike yi wa uwar mijinki wowwww. Na zata mahaifiyata ce kadai uwar miji ta gari ga matan 'ya'yanta."

Kara karanta wannan

“Auren Nan Ba Zai Yiwu Ba”: Uba Ya Ba Kowa Mamaki a Wajen Bikin Diyarsa, Ya Fashe Da Kuka Wiwi a Bidiyo

Uba ya fashe da kuka a wajen shagalin bikin diyarsa

A wani labarin, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan ganin wani uba da ya fashe da kuka harda yayin da ake shagalin bikin diyarsa da sahibinta.

Mutumin ya kalli idanun diyar nasa kuma nan take zuciyarsa ta karaya har sai da ya zubar da hawaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel