Rahoto: Afirka Ta Kudu, Masar, Najeriya da Wasu ’Yan Kasashe 2 Ne Ke Rike da Sama da 50% Na Arzikin Afirka

Rahoto: Afirka Ta Kudu, Masar, Najeriya da Wasu ’Yan Kasashe 2 Ne Ke Rike da Sama da 50% Na Arzikin Afirka

  • Legas, Johannesburg, Cape Town da Nairobi ne ke da kaso 50% na dukiyar da ke dankare a nahiyar Afrika
  • Wani sabon rahoto ya bayyana cewa wadannan biranen ke da manyan attajiran da ke biliyoyin kudade mallain kansu
  • Hakazalika, kasashe irinsu Mauritius, Rwanda da Sychelles ne kasashe masu saurin tasowa a fannin kasuwanci a yanzu

Wani sabon rahoton Henley & Partners tare da hadin gwiwar New World Wealth ya ce, dukiyar attajirai a Afrika ta dara $2.4trn, tare da bayyana birane biyar na nahiyar da suka mallaki 50% na dukiyar Afrika.

BusinessInsider ta ce, wadannan biranen sun hada da Johannesborg da Cape Town a Afrika ta Kudu da Alkahira ta Masar da Legas ta Najeriya da kuma Nairobi ta kasar Kenya.

Attajiran Afrika na kara yawa
Wasu daga attajiran Afrika | Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

An ruwaito cewa, wadannan biranen ne ke da kaso 56% na attajiran da suka fi kowanne dan taliki kudi a nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Yakin Sudan: Peter Obi Ya Yi Tuni 1 Mai Muhimmanci Ga Shugaba Buhari

Masar ke da mafi yawan attajirai a Afrika

A cewar rahoton, a halin yanzu akwai masu hannu da shuni 138,000 da suke da jarin akalla dala miliyan 1 ko sama da haka, da wasu karin 328 da suka mallaki sama da miliyan 100 na dala ko sama da haka, da masu tarin biliyoyin daloli akalla mutum 23.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya bayyana cewa Afirka ta Kudu na da yawan masu kudi sau biyu fiye da kowace kasa ta Afirka, wanda ya kai kashi 30% na masu akalla $100m a nahiyar.

Sai dai kasar Masar ce ke da mafi yawan attajirai a Afirka masu tarin biliyoyin daloli.

Shugaban rukunin kamfanoni masu zaman kansu na Henley & Partners, Dominic Volek, ya ce kasashen Afirka da dama za su fara jan hankalin attajirai ta hanyar ba ‘yan kasa damar zuba jari da zai iya canza tattalin arzikinsu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Buhari Ya Fadi Lokacin Da Yan Najeriya Da Ke Zaune a Sudan Za Su Fara Dawowa Kasar

Rahoto ya yi tsokaci ga yankuna masu tasowa a fannin kasuwanci a Afrika

Rahoton ya kuma bayyana cewa, akwai kasashe masu tasowa a Afrika da ka iya fara tashe a fannin kasuwanci, wadanda suka hada da Rwanda, Mauritius da kuma Seychelles, kuma sun fuskancu habakar dukiya da 70%, 69% da 56 cikin shekaru 10.

Ana sa ran Mauritius za ta ga karin attajirai da kaso 75% a cikin shekaru 10 masu zuwa, inda kasar za ta zama mafi saurin habaka a fannin attajirai bayan Vietnam, India da New Zealand.

Ana kuma sa ran Namibia za ta shaida karin arzikin attajirai zuwa sama da 60% a cikin shekaru goma masu zuwa, bayan da kwanan nan ta kaddamar da tsarin zama dan kasa ta hanyar saka hannun jari don jawo hankalin attajirai.

Hakanan, ana sa ran yawan attajirai a Afirka zai karu da 42% cikin shekaru goma masu zuwa. Afirka na da wasu kasuwannin da suka fi saurin bunkasa a duniya, wanda hakan ya sa ta zama madakatar attajirai.

Kara karanta wannan

Dan Allah a Kawo Mana Agaji, Kasashe Na Ta Kwashe Mutanensu Ban Da Mu", Dalibar Najeriya Da Ta Makale a Sudan Ta Koka

Tuni dama an fara samun sabbin attajirai a nahiyar ta Afrika da ake yiwa kallon na cike da tsananin talauci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel