Mazauniyar Amurka Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Dawo Gida Ta Ga Lalataccen Gidan Da Dan’uwanta Ya Gina Mata

Mazauniyar Amurka Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Dawo Gida Ta Ga Lalataccen Gidan Da Dan’uwanta Ya Gina Mata

  • Wata matashiya yar Najeriya ta fashe da kuka da dawowarta gida bayan shafe shekaru da dama a kasar Amurka
  • Yayin da take Amurka, ta yi ayyuka iri-iri sannan tana ta aikowa dan uwanta na jini kudi don ya gina mata gida
  • Ga mamakinta, ta ziyarci wajen da ake ginin tana sa ran ganin kammalallen gida mai hawa biyu amma sai taga kango

Wata matashiya yar Najeriya da ke zama a Amurka ta karaya bayan ganin gidan da dan uwanta ya gina mata.

A cikin wani bidiyo da aka gano a Twitter, matashiyar ta yi bayanin cewa tana ta aikewa dan uwanta mai suna Obinna kudi domin ya gina mata gidan bene mai hawa biyu kuma da alama ta gamsu da rahoton da ta samu.

Matashiya na kuka a gaban wani kangon gini
Mazauniyar Amurka Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Dawo Gida Ta Ga Lalataccen Gidan Da Dan’uwanta Ya Gina Mata Hoto: @Leopantro
Asali: Twitter

Sai dai kuma, lokacin da ta ziyarci wajen ginin bayan shafe shekaru a Amurka, sai ta ga wani kangon gida.

Kara karanta wannan

“Ya Siya Gidaje, Motoci, Ya Tura Mutane Umrah”: Mai POS Ya Kashe Miliyan N280 Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure

Ta tsinewa Obinna sannan ta sha alwashin hukunta shi kan cin amanarta da ya yi da kuma wawure mata kudinta da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiyar ta koka kan yadda ta kula da Obinna don kawai kada ya taba kudin ginin da ta aiko masa amma duk da haka ya cuceta.

"A kullun ina tura maka da iyalinka kudi don kada ka bata mun harkata amma sai da ka bata mun kayana."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Inno4Chi ya ce:

"Na tuna yadda dan autan abokiyar kasuwancina (da ke zaune a US), mai shekaru sama da 70, ya siyar da gidanta mai hawa biyu a Trans Ekulu, Enugu. Na kai kara gaban EFCC don kwato gidan amma abun takaici abokiyar huldar tawa bata ci gaba ba, saboda son da take yi wa dan."

@chy_omalicha ta ce:

Kara karanta wannan

“Soyayya Bata Tsufa”: Tsohuwa Mai Dogara Sanda Ta Amarce Da Sahibinta, Bidiyon Ya Yadu

"Lokacin da nake yaro, wani gaye ya yi wa yayana irin wannan, ya yi amfani da gumin yayana wajen samun sarauta, lambar yabo sannan yana ta rayuwar kasaita.
"Dukka kudaden da yake samu yana tura yana tura masa.
"Yana ta daukar hoton ginin sauran mutane yana aika masa."

@okey_echezona ya ce:

"Abun ya yi muni sosai, amma akalla lokaci zuwa lokaci, ki dunga tambayar bidiyonyinsa a wajen, hotuna. Ki tura abokai da sauran dangi su dunga ziyartan ginin suna baki bayanin abun da suka gani."

Yan sanda sun kama mai POS bayan ya kashe kudi da aka tura asusunsa bisa kuskure

A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi da ke sana'ar POS ya shiga hannun hukuma bayan ya kashe kudi naira miliyan 280 da aka aika asusun bankinsa bisa kuskure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel