Tufafin Budurwa Ya Kama Da Wuta a Wajen Liyafar Zagayowar Ranar Haihuwarta, Bidiyon Ya Yadu

Tufafin Budurwa Ya Kama Da Wuta a Wajen Liyafar Zagayowar Ranar Haihuwarta, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani hazikin ma'aikacin wajen siyar da kayan makulashe ya sace zukatan jama'a bayan ya shawo kan wani annoba da ya taso
  • Ma'aikacin ya gaggauta daukar mataki bayan wata matashiyar budurwa da ke bikin zagayowar ranar haihuwarta ta kusa babbakewa
  • Mutane da dama sun caccaki matashiyar kan yadda ta bayar da fifiko ga soshiyal midiya fiye da bikin zagayowar ranar haihuwar tata

Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno lokacin da wata budurwa da ke bikin zagayowar ranar haihuwarta ta kusa kama da wuta ta sanadiyar kek dinta.

Da take wallafa bidiyon a TikTok, matashiyar mai suna Big K ta ce ta kasa yin magana saboda tsananin mamaki sannan ta jinjinawa ma'aikacin wajen siyar da kayan makulashen.

Liyafar bikin zagayowar ranar haihuwa
Tufafin Budurwa Ya Kama Da Wuta a Wajen Liyafar Zagayowar Ranar Haihuwarta, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @kimm_ldnn
Source: TikTok
"Mamaki ya hana ni yin magana. Godiya ga wannan ma'aikaci mai kirki da ya yi amfani da hannunsa wajen ceto ni. Ban kone ba kuma tufafina na nan lafiya duk mun yi dariya bayan nan," ta rubuta.

Kara karanta wannan

"Girmanki Ne": Bidiyon Yadda Matar Aure Ta Ki Yarda Ta Shiga Gaban Motar Mijinta Don Karrama Surukarta Ya Tsuma Zukata

A cikin bidiyon, matashiyar ta mayar da hankali sosai kan wayarta ta yadda ta kusa cin karo da ma'aikacin wanda ke shirin ajiye mata kek dinta kan tebur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin haka ne sai kasan hannun riganta ya kama wuta daga kendir din da ke saman kek din. Ma'aikacin ya gaggauta amfani da hannunsa wajen kashe wutan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Davante Wilson ya ce:

"Ya kamata mutane su koyi yadda za su iya yi ba tare da amfani da wayarsu a koyausge ba."

Dani_prettygirl ta ce:

"Wannan shine abun da nake kira da ma'aikacin wata saboda ya yi aiki cikin sauri ya kamata ya samu karin albashi."

heR3alKisha no Clone ya ce:

"Ya ceci ta ita da kek din cikin ban mamaki."

Kelly Princess ta ce:

"Abun mamaki ne yadda ta ki rabuwa da wayar har a lokacin da take babbakewa."

Vee ta ce:

"Wannan ne dalilin da yasa manya suke magana a kan kodayaushe muna rike da waya."

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda makaho ya shige soyayya da tsaleliyar budurwa, ya nemi aurenta

Matashiya ta kama bacci tana tsaka da tuka motarta kirar Tesla

A wani labarin kuma, wata matashiya ta bai wa mutane da dama mamaki bayan bayyana bidiyonta tana sharar bacci yayin da take tsaka da tuka motarta kirar Tesla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng