Gwamnan PDP Ya Zama Na Farko da Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Zuwa N70,000

Gwamnan PDP Ya Zama Na Farko da Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Zuwa N70,000

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin da za a riƙa biyan ma'aikata a jihar
  • A wurin kaddamar da sabon ofishin kwadago a jihar Edo, gwamnan ya ce sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu, 2024
  • Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar kwadago ta ƙasa ke ta fafutukar ganin gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashi saboda tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar Edo.

Gwamna Obaseki ya sanar da haka ne yayin kaddamar da sabon ofishin ƴan kwadago na jihar Edo ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Tsohon ma'aikacin CBN ya fallasa yadda ya karbowa Emefiele cin hancin Dala 600,000

Gwamna Godwin Obaseki.
Gwamna Obaseki ya sanar da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Facebook

A cewarsa, mafi karancin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Mayu, 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ke fafatawa da gwamnati kan ƙarin mafi karancin albashi.

Meyasa Obaseki ya ɗaga mafi karancin albashi?

Matakin ya janyo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya amma gwamnan ya ce da faduwar darajar takardun Naira da kuma tsadar rayuwa ne ya sa ya ƙara albashin Channels tv ta tattaro.

"Ya kamata mu fahimci lissafin, a 2011 lokacin da mafi ƙarancin albashi N18,000, ana musayar kuɗi kan N160/$, wanda ya sa ma'aikata ke samun $120.
"Da nuka ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N40,000 a 2022 ana musayar kuɗi kan N450/$, wanda ya sa ma'aikata ke karɓan kusan $96 a wata."

Kara karanta wannan

An sanya ranar fara binciken Abdullahi Umar Ganduje a Kano

"A yau, 2024, mafi karancin albashi na N70,000 muna musaya a Naira 1,257/$, wanda ya sa suke karbar $55 ƙasa da kashi 50 cikin 100 na abin da suke samu kusan shekara guda da ta wuce.

- Godwin Obaseki.

Ganduje ya caccaki NNPP

A wani rahoton kuma, Dakta Abdullahi Ganduje ya soki shugabannin NNPP inda ya zarge su da shirya makircin tsige shi daga shugabanncin APC.

Shugaban na APC na kasa ya bayyana jagororin NNPP mai adawa a matsayin waɗanda ta kare masu a fagen siyasa kuma duk sun gaza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel