Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa

Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa

- Hukumar 'yan sandan jihar Legas sun damki wata yarinya 'yar shekara 19, ranar 18 ga watan Nuwamba

- An kama Jemila da kawarta wacce ta raka ta bisa zargin bankawa gidan tsohon saurayinta wuta, saboda zafin kishi

- Dakyar aka samu aka ceci sabuwar budurwarsa dake zaune a gidan, wacce dakyar asibiti suka ceto rayuwarta

Hukumar 'yan sandan jihar Legas, ta kama wata yarinya 'yar shekara 19, mai suna Jemila Ibrahim da kawarta, Fatima Mohammed, mai shekaru 21 dake Monkey Village wurin Festac Area a Legas.

Ana zarginta da banka wa gidan wani Mohammed Yusuf na Monkey Village a Legas, wacce budurwarsa Rabi, take zaune a gidan, a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, ya ce Mohammed tsohon saurayin Jemila da ya ji labarin aukuwar lamarin, yayi gaggawar shiga gidan don ya ceto Rabi, sabuwar budurwarsa.

Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa
Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Ya gaggauta kai ta Asibiti, inda aka samu aka ceci rayuwarta da kyar a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

Mohammed ya zargi tsohuwar budurwarsa, Jemila Ibrahim da miyagun halaye kafin su rabu, tukunna ya hadu da Rabi, suka fara soyayya har kaddara ta afka mata.

Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa
Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Yanzu haka 'yan sanda sun kama Jemila Ibrahim da kawarta, Fatimo Mohammed ta Monkey Village, wacce ta raka Jemila wurin yin aika-aikar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas, CP Hakeem Odumosu, ya umarci a mayar da al'amarin bangaren binciken manyan laifuka na jihar, don a yi bincike da kyau.

KU KARANTA: Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako

A wani labari na daban, a daren ranar Asabar ne wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram mai suna Kabir Idris Kura ya wallafa bidiyon wani masallaci da aka fara gininsa tun daga tushe har aka kammala shi.

Bawan Allan ya wallafa, "Alhamdulillah, wannan ne masallacin da jaruma Hadiza Gabon ta ginawa bayin Allah domin yin sallah fisabilillah.

"Ginin ya kammala kuma muna mata addu'ar Allah ta'ala yasa mata a mizaninta, ya kuma saka mata da alkhairi, ya ji kan mahaifinta Malam Aliyu Diya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng