“Na Rasa Dangina Saboda Na Auri Dan Najeriya”: Uwa Mai ‘Ya’ya 4 Ta Ba Da Labarin Kanta
- Wata mutuniyar kasar Afrika ta kudu ta magantu kan yadda aurenta da dan Najeriya ya shafi alakarta da yan uwanta
- Uwar 'ya'ya hudun ta rasa danginta amma ta yi ikirarin cewa sun yi kokarin kashe mata aure ne
- Ta aika gagarumin sako ga mazan kasarta game da yan Najeriya yayin da mutane da dama suka yi martani ga wallafarta
Wata mata mai 'ya'ya hudu ta bayyana cewa ta rasa danginta daboda aure wani dan Najeriya.
Matar mai suna @iamarealpearl a TikTok, ta ce danginta sun yi fafutuka don ganin aurenta ya mutu.
A cewarta, sun nemi taimakon jama'a sannan suka tsara labaran kanzon kurege don ganin sun rasa damar kula da yaransu.
Sai dai kuma, matar yar kasar Afrika ta kudu, ta nuna soyayyarta ga mijinta dan Najeriya sannan ta shawarci mutanen Afrika ta Kudu da su daina kyamar yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa ba dukka yan Najeriya bane miyagu sannan ta kara da cewar kimanin shekaru 10 kenan da suka yi gwagwarmayar da danginta.
Wallafar tata ta haifar da muhawara a dandanin na soshiyal midiya.
Kalli wallafarta a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Yvonne Maqhula ta ce:
"Ki ji dadin aurenki kin ji sannan ki so mijinki, wadanda ke jiranki ki dawo da kuka za su yi ta jira har sai idanunsu sun zama ja."
@user5324279836152 ya ce:
"Duk kasashe suna da mutanen kirki da ba banza. ki yi addu'an samun nagari. ki mallaki mutumin sannan ki yi farin ciki."
@user4618599173526 ya ce:
"Magana ta gaskiya tun da har dan Najeriya ya auri yar Afrika ta kudu ba karamin kokari ya yi ba fa saboda yawancin mazan Najeriya ba za su aikata haka ba."
@African child ta ce:
"A kodayaushe ina fadama mutane cewa ina da abokai yan Najeriya wadanda suka cika da soyayya kuma idan kana tare da su za ka ji kana da kariya amma wasu mutane sun tsane su."
@Vic ta ce:
"Duk daya suke amma ina maki fatan alkhairi ina dai fatan kin ziyarci Najeriya ba wai kawai ki tsaya a nan Afrika ta kudu ba,,,ki ziyarci danginsa."
A wani labari na daban, mun ji cewa wata kyakkyawar budurwa ta amarce da wani mutumi da ya raineta tun tana yar karamar yarinya a wani kasaitaccen biki.
Asali: Legit.ng